Sunday, 18 November 2018

DIY BODY WASH | YADDA AKE SABULUN WANKA | Rahhajs DIY

a wanna videon zakuga yadda zaku hada sabulun wanka da kanku a gida cikin sauki, wanna sabulun wankan yanadamatukar alfanu ga fatarmu domin yana kunshe da sinadarai ne na gargajiya wanda suke hyara fata su sanya shi haske, walkiya da kyau a cikin dan kankanin llkaci.

Tuesday, 6 November 2018

HOME MADE GARAM MASALA | YADDA AKE SINADARIN DANDANON GIRKI | Rahhajs DIY

 In this viseo i will be showing you how to make a quick and easy garam masala spices. garam masala is an indian mix spices that is made with whole spices that are been roasted and grinned. if you try this easy garam masala i make you will never buy want to buy from store again. with this spices, you can elavate your cooking to a whole new level. so is you wanna learn how to make it, please watch the full video tutorial, remember to like and subscribe to my channel to support me, thank you.

Monday, 15 October 2018

RAHHAJ,S GIFT SHOP/yadda nake Sana'ata

domin samun kayyayyaki na gudunmawar aure, barkar haihuwa ko bada wata kyauta ta musamman, maza ku dnna wannan videon dan kallon irin kayatattun kayayyaki da muke dasu na alfarma dai dai da aljihunku.

Sunday, 7 October 2018

Thursday, 20 September 2018

FULL FACE MAKEUP TUTORIAL/ Yadda ake kwalliya

A wannan videon namu nayau zakuga yadda ake ake kwalliyane daga farko har karshe, zamu nuna aku abubuwan daya dace kuyi anfani dashi ayayin da zakui kwalliya da kuma abubuwan da basu dace kuyi anfani dashi ba. kuna iya ajiye tambayoyinku a kasan comment box na videon nan domin mu baku gamsashshen amsa.

Thursday, 13 September 2018

YADDA ZAKU HADA JAMBAKI DA KANKU A GIDA

Assalamu alaikum , am back today with this amazing tutorial on how to make lip stick at home, wannan jan bakin (lip stick) da zan nuna maku yau zan hadashi ne ta hanyar anfani da mai wato jelly sai kuma kala wato crayon. the first thing to do is to melt the crayon with the vasiline in a double boiler, ku barshi ya narke sannan sai ku jiye cikin kwalbar janbakin ku barshi ya huce. kyna iya danna videon dan kuga yadda nayi,.https://youtu.be/1veL8eL_Ggw

Wednesday, 5 September 2018

YADDA ZAKUYI MAN KITSO (MAGANIN AMOSANI)/Anti dandruff hair cream

Assalamualikum, barkanmu da sake saduwa acigaba da kawo muku dabarun harhada abubuwa da kanku agida, Ayau in sha Allah zan nuna maku yadda xakuyi man gyaran gashine wanda zai magance maku amosani ta hanyar anfani da ganyen darbejiya.

  abubuwan da zamuyi anfani dasu sun hada da man kadai, man jelly sai castor oil. Castor oil daban ne da man gelo ko man kadai kamar yadda wasubke fada. Anma kuna iya duba videon ta wannan link din dan ganin yadda yake https://youtu.be/1IY2UKZPGUI

Da farko zaku hade mayukanne a cikin mazubi guda, saiku daura akan ruwan zafin da yake kan wuta (wato double boiler) ku dannan link din nan dan ganin yadda zakuyi https://youtu.be/1IY2UKZPGUI kamar dai yadda na koya maku in zakuyi man shafawa, da man lebe. Sai kuyi ta juyawa har sai gaba daya launinsa ya canza saiku sauke in ya huce ku juye a kwalba.
  Wannan man yanada anfani sosai kamar yadda na lissafo acikin videon. Idan akwai mai tambaya ku ajiye a kasan videon inna bude zan baku amsa. Ga link
https://youtu.be/1IY2UKZPGUI

Sunday, 2 September 2018

SIRRIN GYARAN JIKI/GASHIBDA MAN DARBEJIYA, DA YADDA ZAKI HADA MANSA A GIDA

Assalaualaikum yan uwa barka da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cigaba da kawo maku darussa na yadda zaku rika harhada abubuwa dakanku a gida kuma cikin sauki.
  A rahhaj diy na yau zan nuna maku yadda zaku hada man darbejiya ne dakanku cikin dan kankanin lokaci. Man darbejiya yana da anfani sosai domin yana magance cututtuka da dama kamar malaria da taipod. Bayan nan ana anfani dashi wajen magance matsalolin fata kama daga kurajen jikibda pimples na fuska. Sannan ana anfani da shi wajen gyaran gashi domin ya kasance daya da ga cikin sanadaren da ake anfani da a kasar india domin hada mayukan gashi daban daban.
  Idan zamu hada man darbejiya akwai bukatar mu tanadi ganyen darbejiya wanda yake bai busheba. Sai mubdaka a turmi, ba a so asa masa ruwa yayin dakawar. Bayan yayi laushi sai asa acikin man kwakwa Sannan asa cikin ruwa a tafasasu tare. Kuna iya duba videon da nai dan ganin yadda nai nawa ta hanyar danna wanan link din https://youtu.be/2T791qaCuZ4. Bayan ya canja kala sai ku tace ku fidda dusan ganyen ku bari inya huce saiku jue man a kwalba ku rufe. Wannan mai in kuna anfani dashi wajen man gashi da kuraje zakuji dadinsa sosai. Anan gaba kuma zan nuna maku yadda zaku hada man kitso wanda zai magance maku amosani in sha Allah.

Wednesday, 29 August 2018

YADDA AKE DINKIN ZANNUWAN GADO

Dinkin zannuwan gado yanxu sun canja salo domin yanzu ana kawatasu fiye da da, wajen yin anfani da yaduka na alfarma dama kananun matasai wanda akafi sani da throw pillows, wayanan kananan matasa suna kawata gado matuka musanmam idan akai anfani da kaloli da siffa kalakala.
  Idan za ai dinkin zanin gado ana fara duba girman gadon da za aiwa wannan zanin gadon, da kuma irin kanshi shi zanin gadon da za ai, wanan yasa zannuwan gado suke kala kala kama daga simple bed spread wanda baida tarkace a jiki da mamai tattara da mai soso da dai sauransu. https://youtu.be/3d2ANKDTqms
  Anma a takaice in za mu dau baanin zanin gado irin wanda akafi anfanibda shi akan gadobkuma wanda sune sukafi yawa wato 6by7 shi ana anfani da yadi 4 ne, yadi 3 zaki kalmashe kiyi zanin gado ragowar yadi 1 kuma ki dinka rigunan filo dasu. Sannan akai zanin gado half set da kuma full set wato wanda sukeda matasai dayawa da kuma soso ko fiber, a wannan video muna tare da kwararriya kuma shahararriya wajen dinkin zannuwan gado anan garin kano, ku dannan link dinnan dan ku anfana da bayananta da kuma abubuwan da ta sanarmana wanda suna daga cikin sirrin dinkin zannuwan gado ga masu sha awar suma su koya https://youtu.be/3d2ANKDTqms

YADDA AKEYIN MAN DARBEJIYA /Sirrin Man darbejiya



ASSALAMUALAIKUM,

A yau rahhajs diy tazo muku da hanya mafi sauki wanda zakubi wajen yin man darbejiya dakanku a gida. man darbejiya yanada matukar anfani ga dan adam, daga cikin anfanunnukansa akwai magance taifod, zazzabi, kuaraje da gyaran jiki musanmam gyaran gashi. awanan videon zakuga yadda zakuyi naku man darbejiyan domin samun wayannan garabasar, sauran bayani yana acikin videon, ku dannan dan ku gani.


YADDA AKE DINKIN LABULE

Assalamualaikum ,barkanmu da sake haduwa a darusanmu da muke kawowa na yadda zaku iya yin dinkibda kuma harhada abubuwa da kanku a gida cikin sauki. Ayau zanyi takaiceccen bayani ne akan dinkin labule. Dinkin labule abune mai sauki in dai an dauki awon taga ko kofar da akeson ayiwa labulen.
  Abu na farko da akeyi shine asan fadin kofar da za aiwa labulen, sai a aina tsayin kofar bayan anyi wannan za a rubuta awon saboda kar a manta sannan sai ku dauko yadin da zakuyi anfani da shibwajen dinkin labulen, saiku auna wannan fadin da kuka auna na kofar taku, to anan idan kunason labulen yayi tattara saikusa awon sau biyu (misali idan kofarku inchi 20 ne fadin, sai kusa inci 40 a yadin sannan saiku yanka, kuna iya sawa sau 1 da rabi ko sau 2, ya danganta da iya tattarar da kuke bukata. Nayi bayani a wannan videon kuna iya danna link din ku kalla https://youtu.be/HZnipJDVoW4
  Sannan idan kukazo wajen yin gidan karfe, shi anasa inci 4 ne gaba daya sannan sai ku raba biyuba tsaye da dinki yadda zai baku inci 2 guda 2. Wato gidan karfe da kuma wannan tattarar ta saman karfen. Wannan awon na bakin karge ne, anma idan karfenki irin mai kaurin nan ne to fa sai kin auna sannan kisa daidai da naki. A wannan videon na nuna yadda na dinka nawa labulen daga farko har karshe , ku danna link din dan ganin yadda nayi nawa https://youtu.be/HZnipJDVoW4

Monday, 23 July 2018

Gyaran jiki da kwai/DIY egg face mask

    A wannan video na yau na duba yadda zamu magance matsalolin fata ne ta hanyar anfani da kwai. domin samun cikakken bayanin akan yadda zaku sarrafa kwai dan samun lafiyayyar fata sai ku danna wannan videon.

Wednesday, 11 July 2018

YADDA ZAKU HADA FILAR KWAI

A yau kuma nazo maku da yadda zaku hada fitilane anma ba irin namu na gargajiya ba, wannan fitilar irin ta zamanice sai dai kuma nayi anfani da dabaru wajen hadata. wato ina nufin nayi anfani da abubuwane wanda suke cikin gidajenmu wajen hada wannan fiitilla. kamar misalin kofi, takarda, da dai sauransu. sai ku biyuni dan ganin yadda nayi wannn fila a cikin videon nan.

Tuesday, 26 June 2018

YADDA ZAKU HADA ABUN HANNU

Hada abun hannu abune mai sauki wanda za ku iyayi da kanku acikin kankanin lokaci, musanmam ma abun hannu wanda akai da dutsen beads.
A wannan karan zan nuna maku hanya mai sauki wanda zaku hada abun hannu mai sauki, domin zakuga yadda nai anfani da abin hannuna wanda ya tsufa wajen hada wani sabo kar maimakon na yarda shi. Wanda hakan ya kara kawata beads din.
  
  Abubuwan da zaku nima

Beads (manya da kanana)
Zaren roba (irin wanda ake shiri da)
Kwallon beza (tensile)
Karfen adon abon hannu (zaku iya anfani da kasan yari Wanda ya lalace)

Da farko zaku dauki tape ku auna hannun da zakuyiwa abun hannun saboda da roba zamuyi, anasone ya kama hannu kar yayi yawa. Bayan an auna sai ku rika iban beads din kuna shirya cikin zaren robarnan. Zaku iya shiryasu yadda kukeso manya da kanana ko manua zalla, kuna shiryawa kuna dan sirkawa da karfen adon nan. In kun gama sai ku kulle sosai yadda bazai ware ba. A wannan videon zakuga yadda na hada nawa, da kuma kalolin da nai daban daban. Ku danna link din nan dan ganin yadda nai nawa.   https://youtu.be/lYWn9suLzB4

Friday, 22 June 2018

YADDA AKE KUNSHI/ HENNA ART





Kunshi wani salone na kwalliya wanda ya samo usuli daga kasashen asia wato gurin larabawa da kuma india, ana yin kunshi ne dan kawata jikin wacce akaiwa musanmmam ga amare da matan aure dan birge mazajensu. a Nigeria yanzu kunshi na daga daya daga cikin ado mafi daukaka yayin da akace ana gudanar da bukukuwa na aure ko na salla. awani lokaci abaya ana anfani da ganyen lallene wajen sarrafa wannan kunshi a inda za a tsinki ganyen lalle a busar sannan a daka, bayan yayi laushi sai a kwaba da ruwa da kuma wasu sinadaren kamar zobo da siga.

   bakin kunshi ayanzu wani salone wanda ake anfanida wajen zanen fulawa a hannu da kafafuwa, wani sain ma har a wasu bangarori na jiki. abin alajabi anan shine bakin lalle ana anfani da wasu sinadarai ne sabanin ainihin ganyen lalle da muka sani na gargajiya. to a wannan videon na kawo maku yadda ake hada bakin lalle da kuma bayanin banbancinsa da ja. sannan a lokaci guda na nuna yadda ake ake zanashi a hannu da kafa. to asha kallo lafia.

Wednesday, 20 June 2018

YADDA ZAKU DINKA LABULE

Dinkin labule abune mai sauki wanda cikin dan kankanin lokaci za a iya yinsa. Labule na daga cikin kayan da suke kawata gidajenmu musanmam in akai anfani da yadi ko launi wanda yai daidai ya kuma haska wannan dakin da akai dominsa. A wannan karan zanyi maku bayanine akan hanyar da zakubi mafi sauki wajen dinkin kabulayenku da kanku a cikin gidajenku.

Abubuwan da zaku tanada.
Yadin labule
Tape mai zare
Tape na karfe ko lura
Karfen labule
Pin da keken dinki.

Yadda zaku dinka.
Da farko akwai bukatar ku auna kofa ko kuma tagar da zaku dinkawa labulen, ta hanyar anfani da tape. Wato zaku auna fadin kofar k nan da kuma tsayinta, dan ganin cikakken bayani akan yadda na auna kuna iya danna wannan link din https://youtu.be/HZnipJDVoW4 . Bayan kun auna Sannan saiku dakko yadin naku, misali in kun auna kofarku a kan inchi 5, to yanada kyau ku ninka awon yadda zai baku tattara bayan kun dinka, sai dai in mutum yafison labulen ya tashi ba tattara, ko da yake in akai mai tattarar yafi kyau.
  Atakaiche dai shi dai fadin kofa ana sa yadi daya ne da rabi zuwa yadi biyu. Tsayin kuma ya danganta da iya tsayin kofarku. Sannan in aka tashi za ai dinkin gidan karfe na labule ana sa inchi 2 ne. A wannan videon nai bayani tare da nuna yadda nai dinkin labulen domin karin bayani. Ku dannan wannan link din, https://youtu.be/HZnipJDVoW4  dan ganin yadda nayi.

Saturday, 2 June 2018

GYARAN JIKI DA KURKUR



 KURKUR wani sinadarine mai matukar amfani jikin dan adam, ana amfani da kurkur wajen yin girki a kasashe daban daban na duniya, musanmam ma kasar india. kurkur yanada launi mai ruwan kwai kuma yana kama da citta sai dai shi baida yaji kamar shi citta. kurkur nada amfani daban daban ciki harda gyaran jiki da sanyawa fata lafiya.

  a wannan videon nayi bayani akan hanyoyi daban daban da za a iya anfani dashi wajen gyaran jiki ta hanyar amfani da kurkur kamar, maganin kuraje, maganin tabo, maida tsohuwa yarinya da dai sauransu.

Sunday, 27 May 2018

MAGANIN GASHI DA ALBASA

https://youtu.be/D0ATnrZCIEU

Ayau in sha Allan zamu duba yadda ake anfanine da farar albasa wajen gyaran gashi. Farar albasa tana dauke da sinadare wanda yake amatsayin abinci na gashi, wanda in har gashi yana samun wannan abinci to zai kasance cikin sheki, da tofo ako da yaushe.
  A wannan videon na nuna yadda zakuyi anfani da albasa wajen karawa gashinku tsayi, baki, kyau da lafiya. Sannan na nunu dakidaki hanyar da zakubi wajen cinma wannan matsayi. Dan ganin yadda zakuyi anfani da farar Albasa dan samun wannan garabasa sai ku danna wannan link din. https://youtu.be/D0ATnrZCIEU

Sunday, 13 May 2018

YADDA ZAKU MAIDA TSOFFIN TAKALMANKU SABBI





Sau dayawa mukan samu damuwa in muka sai sabbin takalma kuma suka sami matsala cikin dan kankanin lokaci. kasancewar bamu da masaniyar hanyar da zamubi wajen gyarawa ko dabarar da zamuyi mu magance faruwar hakan. a wannan videon zan nuna maku yadda zakubi wajen gyara da magance faruwar hakan cikin sauki.
    Abubuwan da nai anfani da wajen gyaran takalmin nan sun hadar da fata, gam da kwali. Kuna iya danna wannan link din dan kasancewa da wannan video yanxu https://youtu.be/Z_qJEL48PTE

Thursday, 3 May 2018

SANAO'IN HANNU A TARON JUMETA FUN FAIR



yadda ta kasance ke nan a taron jumeta fun fair tare da matasa masu kananan sana'oi. taron ya kawatar tareda nishadan tarwa kwarai domin matasa musanmam ma mata sun fito dan bajakolin sana oinsu na hannu.

Monday, 23 April 2018

YADDA AKE HADA FULAWA DA TAKADDA


https://youtu.be/i23BaT9Y6qg
Ko kunsan zaku iya anfani da takadda wajen harhada abubuwa dama, bayan rubutu da muke akai wanda shine babban abu da muka fiyeyi da shi? to Ayau zannuna maku yadda zaku hada fulawa ne ta hanyar anfani da takadda, wannan fulawar da zan nuna maku abune mai saukin hadawa wanda cikin kankanin lokaci zaku hada, kuma ta hanyar anfani da abu biyu kacal, wato takadda da gam.

   wannan fulawa da zamuyi yau yana kawata waje in akai shi cikin launi daban daban musanmam in akai anfani da shi wajen kawata dakunan yara, wajen wasansu da ma cikin azuzuwansu. ku biyoni acikin bidion dan ganin yadda zan hadashi.
https://youtu.be/i23BaT9Y6qg

Friday, 13 April 2018

GYARAN GASHI DA ALBASA




YADDA ZAKU GYARA GASHINKU DA ALBASA

Albasa yana da anfani daban daban ciki harda gyaran gashi, kasancewar sa yana dauke da sinadarin sulfur. sulfur sinadari ne mai matukar mahimmanci ga jikin dan adam musanmam ga gashi. wannan sinadarin sulfur din abune wanda ke karawa gashi lafiya, tsayi ,baki, sheki sannan kuma ya maganche duk wasu ire iren cututtuka da sukan addabi gashi kamar amosani, sanko da sauransu.
 a wannan bidion nayi bayanin anfanin farar albasa ga gashinmu tare da nuna hanyar da za'abi wajen hada sinadarin da zai gyara maku gashinku da albasar.

Tuesday, 6 March 2018

YADDA ZAKU DINKA TUM-TUM (1)



Assalamualaikum yan uwa, barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa a cigaba da kawo maku dabarun harhada abubuwa da kanmu acikin gidajenmu kuma acikin sauki . Ayau zamuyi bayani ne akan yadda zakuyi tum tum, wato manyan filo wanda ake ajewa a cikin daki akasa. Wannan tumtum kala kala ne amma zamu fara bayani akan wanda yafi ko wanne sauki in yaso daga baya, sai muyi bayani akan sauran in sha Allah.

Abubuwan da za'a tanada
Yadin kujera ko wani yadi mai dan kauri
Fiber ko crumbs (soson katifa)
Tape
almakashi
Zip
Yadda zaku dinka
Dafarko zaku fara auna iya girman da kukeso wannan tumtum ya kasance. Misali ni anawa nasa tsayi inci 22 fadi kuma inchi 20. To kuma kuna iya sa hakan ko ku kara ko ku rage.
Sai ku sa almakashi ku yanka dai dai abinda kuka auna, inkun tashi yankawa zakunyanki guda 2 ne, wato gaban filon da bayan. sannan saiku hadesu biyun. Ku kama saman ku dan dinke, kasanma ku kama ku dinke (misalin inci 2) akwai video da nayi dan karin bayani sai ku danna wannan link din https://youtu.be/J56Dvtm4gdo dan ganin yadda zaku kama ku dinke.
Bayan kun dinke saiku bude wanan yadi yadda zai tashi guda daya. To anan zakuga tsakiyan yadan bude kamar fuskar nikabi. To tanan ne zamu saka zip. Yanzu sai a dakko zip din a sanya ta kasan wannan fuska da mukai a kama gefe gefen a hada da jikin zip din a dinke. (wanan waje yanada wuyar bayani da baki shi yasa na aje link dan kuga abinda nake nufi yayin dinkewa https://youtu.be/J56Dvtm4gdo. Ku danna kuga yadda nasaka zip din)
To bayan ansa zip din saiku juya yadin abaibai ku take ragowar gefen guda uku. Zakuga ya hade ya baku suffar pillo. To saiku bude zip din ku juyo da shi dai dai. To anan zaku iya anfani da fiber ko foam wajen duri, sannan zaku iya sa fiber kai tsaye aciki ko ku fara dinka wani gidan pilon ku dura fiber aciki kafin kusa acikin tumtum din. Sannan in kunaso zaku iya samun foam inci daya ku manne gefen guda hudu da gam ku dura crumbs aciki (ku duba videon na nuna wannan kalan)
  To da kunyi wannan shikenan sai ku zuge xip dinku. Shi 4thum tum anayinsa hawa hawane, kamar hawa 2,3 ko 4. Ya dangsnta da raayin maishi. To in kun tashi zakuy karamin wannan saiku rage inchi 3 zuwa 5 akan wannan awon da na baku, in kuma zakuyi banbansa saiku kara inchi 3 zuwa 5 akan awon.
Wannan shine yadda zakuyi tum tum.mai sauki. Karku manta ku danna wannan link din dan ganin komai acikin video. https://youtu.be/J56Dvtm4gdo

Monday, 5 March 2018

YADDA ZAMU GUJEWA KURAJEN FUSKA (PIMPLES)




Assalamualaikum yan uwa munai maku barka da kara kasancewa damu. In sha Allah yau zamu dora bayaninmu da mukeyi akan kurajen fuska, a baya mun nuna hanyar da muyi mu magance kuraje a fuskarmu, ayau kuma kamar yadda na alkawarta zanyi bayani akan abubuwan da ya kamata mu kiyaye domin ganin mun rabuda kurajen da suke damun mu in sha Allah.
1) YAWAITA WANKE FUSKA
dayawanmu muna da dabi'ar yawaita wanke fuskokinmu akai akai, wasu sukan wanke fuskarsu a rana akalla sau 6 ko fi kuma da sabulu. Wannan dabi'a tana kara janyo mana kuraje a fuskarmu saboda wayannan sinadaren da suke cikin sabulun suna wanke ainihin maikon da Allah ya sanya fata ta kasance ciki sannan su sa fata bushewa da kuma darewa.
  Abinda ya kamata mu yi shine indai zamusa sabulu a fuskarmu to akalla mu wanke sau 2 kawai (safe da yanma/dare).
2) ANFANI DA SABULU MAI KARFI
dayawanmu mukan yi anfani da sabulu wanda yafi karfin fatarmu, misali medicated ko lightening soap. Wayannan suna dauke da sinadaren da suke kara sanya wa fuska ta samu matsalar fata musanmam ga wayanda dama can sunada pimples a fuskarsu, maimakon wayanan sabulai zaifi kyau mu samu sabulu wanda yake baida karfi sosai (beauty soap kamar joy, giv, dov, lux etc) anma matukar zamu cigaba da anfani da sinadarai masu karfi akan fatarmu to ko muna maganin kuraje, zasu rika tafiya suna dawowa.
3) MAN SHAFAWA MAI KARFI
man shafawa kamar sabulu shima, yana dakyau mu nimi wanda yayi daidai da yanayin fatarmu. Misali in fatarmu mai saurin bushewa ce to yana da kyau mu nimi man shafawa mai dan maiko wanda zai rika hana fatarmu saurin bushewa da tsagewa. Haka in fatarmu mai maikoce, to zaifi kyau muyi anfani da mai wanda baya daskarewa jikin fuska saboda fatar ta samu damar shan iska yanda ya kamata.
4) KWARZANE FUSKA /FASA PIMPLES
wannan dabi'a ita tafi saurin janyo mana matsalar kuraje da kuma tabbuna a fuskokinmu, dayawan masu fama da pimples basa rabo da wasa da hannunsu akan fuskokinsu, kodai suna shafa fuskar ko kuma suna fasa pimples din ko suna kwarzane kurajen. Wannan yanasa kwayoyin cututtka saurin shiga fata wanda yana daya daga cikin dalilan da suke kawo pimples, sannan yana sa kurajen suyi baki su bar mana alamar tabo wanda yakan dauki lokaci kafin ya fita.
5) RASHIN WANKE HANNAYE AKAI AKAI
Barin dauda ajikin hannu yana taimakawa matuka wajen kara jawo mana pimples a fuskokinmu, shi yasa yake da kyau mu rika wanke hannayenmu kafin mu shafa mai ko wani maganin kuraje saboda da tafin hannunu muke yin kusan komai kama daga shara, ayyukan gida, taba wayoyinmu da dai sauransu,shiyasa in muna wanke hannu akai akai sai mu guji karawa ciwo ciwo.
6) RASHIN GYARAN FUSKA (DILKA)
Rashin gyaran fuska wanda zai taimaka wajen cire duk wani dauda da take kan fatar mu na taimakawa wajen kara jawo mana kuraje, kamar yadda yawaita yin gyaran fuskarma zaibiya kara mana pimples a fuskokinmu. Dilka ko exfoliating hanyace da akebi wajen cire duk wani datti da mataccen fata wanda baida anfani akan fatarmu, ta yadda fatar tamu zata kasance da kyau, sheki, tsantsi da lafiya a koyaushe. Shi yasa yake da kyau mu rika yawaita yin wannan akalla sau daya a sati domin mu hana sabbin kuraje baiyana a fuskokinmu.
7) YANAYIN ABINCHI
Abincin da muke ci yana daya daga cikin abinda yake kara jawo mana kuraje a fuskokinmu, kamar yadda mukasani yawaitar maiko a karkashin fata na daya daga cikin dalilan da suke kawo mana kuraje, shi yasa yake da kyau mu rika ragewa koda bazamu iya daina cin nauoin abinchin da suke dauke da maiko mai yawa wanda suke jawo mana pimples ba. Misalin abincin su hadar da kayan zaki irinsu cake, doughnuts, da dai sauransu, sai kuma masu maiko kamar gyada, magerine da dai sauransu.
8) SHIGA RANA
Yawaita shiga rana na daya daga cikin dalilan da yake sawa muyita maganin pimples anma yaki tafiya koda kuwa muna bin dokoki muna kiyaye cimarmu. Shiyasa mafi akasarin masu fama da pimples yan matane wayanda suke yawaita fita makaranta, aiki da dai sauransu. Yana da kyau in za a fita cikin rana kar a shafa mai wanda yake da maiko sosai (oil) ko kuma ayi anfani da man kariya (sunscreen)
9) YANAYIN HALITTA
Bayan duk wayannan dalilai dana lissafa a sama akwai kuma wanda dama halittarsu ce kurajen fuska, wannan kuma yana faruwa ne saboda rashin daidaitar sinadaren halitta na jiki (homones) shiyasa wasu za kuga suna iyakar kokarinsu wajen kiyaye duk wayannan sharudodi anma duknda haka pimples baya rabuwa da fuskokinsu. Wayannan abunda ya kamata shine su nimi likita dan ya sanar masu da kwayoyin da ya dace suyi anfani da shi wajen magance matsalar.
10) LOKACHI
Pimples lokacine kamar yadda dayawan mutane suke fada, koda yake wasu harda rashin kiyayewa da bin sharrudan da na lissafa, anma mafi akasarin lokuta pimples yana zuwa ne dai dai lokacin da matasa suke samun yanayin canji na girma a halittarsu :puberty
Sai dai wasu daga nan ne kuma in basa kiyaye sharudan nan na sama sai su wuce dashi har girma.
11) BLEACHING
Bleaching ko shafe shafe na daya daga cikin manya manyan dalilan da suke kawo kuraje jikin fuska, kuma wannan shi yafi ko wanne muni domin shi zai futo manya manya sannan yasa fuskar tai jirwaye ta kuma yi tabbuna ko ina, shi yasa yana da kyau mu guji anfani da duk wani mai ko sabulu da zai sanyamu haske domin suna kona mana fatane kawai su kuma baiwa cututtuka damar shigar mana fata.
Wayannan sune kadan anma kuma manya manyan dalilan da suke jawoana kuraje a fuska ya zamana munata magani anma bama samun canji, da fatan zamu kiyaye. In sha Allah nan gaba zamuyi bayanin kalolin dilka da yadda zamu hadasu da kanmu cikin sauki .

Wednesday, 28 February 2018

YADDA ZAKU MAGANCE KURAJEN FUSKA (PIMPLES)



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da warhaka, ayau in sha Allah zamu duba daya daga cikin abubuwan da suke damun mafi akasarin mata musanman yanmata da mata masu karancin shekaru, Wannan abu kuwa shine kurajen fuska wanda ake kira da pimples.
 
Abubuwan da za'a tanada
Ruwan dumi
Sabulu
Lemon tsami (lemon)
Baking soda
Man zaitun.
Yadda zakuyi
Dafarko zaku samu ruwan dumi saiku wanke fuskarku da sabulu da wannan ruwa mai dumi.
Sai ku samu tawul ko wani yanki mai kyau ku goge fuskarku da shi.
Sai ku dauki lemon tsami (lemon) in babu sai kuyi da (lime) ku yanka gida biyu ku dauki rabin ku matse ruwan ku hada da baking soda (wannan dabanbanci da baking powder) misalin rabin karamin cokali saiku kwaba da kauri, sai ku shafa adaidai inda kurajen suke.
Sai ku barshi jikin fuskar sai ya bushe, bayan misalin minti 10 saiku dauki ruwa ku wanke fuskar dashi. Sannan sai ku goge da tawul ku shafa man zaitun.
Haka zakuyi kullum ko akalla sau 4 a sati. In sha Allah zakuga kurajen suna motsewa.
Wannan hanya in sha Allah in aka gwada za a dace, anma dole sai an kiyaye wasu halayya da mukeyi wanda mafi akasari yin hakan shine yake sawa kurajen su rika futowa. A gobe in sha Allah zamuyi bayani akan wannan halayya da muke da kuma hanyar magancesu.

Tuesday, 27 February 2018

YADDA ZAKU HADA JAKAR PAS (marar dinki)



 Ayau ma kamar yadda muka saba munxo maku da yadda zaku hada jakar hannu ta mata mai sauki wanda zakuyi ba tareda kunyi dinki ba, wannan jakar batada wuya kuma bata bukatar keke wajen hadata.
Abubuwan da zaku tanada
Cushion/mako/malha
Kwalin magwaji
Leda/fata
Yadin shafin jaka/satin
Maballi
Wuka
Gam
Almakashi
Zip (ba dole bane)
Yadda zaku hada
Dafarko zaku dauki kwalin magwaji sai ku yanka irin shape din da kukeso pas din ta bayar. Misali zaku dauki kwalin saiku lankwasa ta gida 3, kamar dai pas, to furkar saikusa almakashi ku yanka a karkace ko a gewaye.
  Bayan kunyi wannan saiku dakko malha ko cushion inchi 1 ko inchi 2 saiku dora wannan kwalin akai ku shata ku sa almakashi ku yanka sai ku ajiye a gefe.
  To sai ku dakko kwalin nan ku daura akan fatar/ledar da zakuyi jakar kusa biro ku shata, sannan saikusa almakashi ku yanke, anma in zaku yanke bazaku bi ta kan biron ba zaku dan matsa kadan misalin ½ichi.
  To shima yadin shafin haka zaku yankashi dai dai da wannan fata ko leda da kuka yanka. Sai ku dakko malhar nan ko cushion ku shafa mata gam shima fatar/ledar da zakuyi jakar ku shafa gam. Saiku ajiye ku bari ta bushe. In kun taba kunji baya kama hannu saiku mannesu waje daya (zakuga fatar yadanfi girma saiku lankwasata ku manne jikin malhan. Ku danna link dinnan kuga abinda nake nui anan acikin videon nan https://youtu.be/Y9ulCYVAzGE)
  To sai ku dakko kwalin magwajin nan da yadin shafin suma ku shafa masu gam, a gefe guda guda, insunsha iska saiku mannesu, shima yadin sai alankwasa ajikin kwalin.
  To yanzu sai mu dakko wannan fatar da malhar da muka manne mu shafa gam ajikin malhar, shima mai yadin shinan da kwali sai a shafa gam ajikin kwalin sai abarshi yasha iska, sannan sai a mannesu (anan yanzu zamu mana maballanmu kafin mu manne gaba daya) zamuyi anfani da wuka mu dan huda sai mu manna) ku danna link din kuga yadda na manna https://youtu.be/Y9ulCYVAzGE
  Yanzu saura cikin jakar. Wannan pas din mai wallet ne shi yasa bama bukatar ai masa makari a gefe, anma nan gaba zan nuna maku yadda zakuyi mai makarinma in Allah ya yarda.
  Sai ku yanko yadi daibdai da fadin tsakiyar pas din (kunsan mun lankwasata gida uku da fari) sai ku yanka yadin gida biyu ta sama kusa zip, anma wannan ba dole bane, in kunaso kuna iya lankwasawa kawai kuyita hawa hawa kamar yadda akeyin maajin id card acikin wallet. Saiku shafa gam a zagayen jakar, iya inda zaku manna aljihun, inya bushe sai ku manna. In kunaso zaku iya dan kara wani yadin yayin mannewa saiku rika sa chain/sarka irin hannun jakar nan na suwaga. Wannan bayanin da nake gaba daya na nunashi dalla dalla acikin videon nan, kudai ku dannan link kawai ku sha kallo https://youtu.be/Y9ulCYVAzGE

Monday, 26 February 2018

YADDA ZAKU DINKA JAKA MAI SAUKI (ba zip ba shafi )





Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa acikin wannan fili namu da muke koya maku yadda zaku harhada abunuwan anfaninku da iyalanku a cikin gidajenku kuma cikin sauki. Ayau zan nuna maku yadda zaku dinka jakane mai sauki, saboda wannan jakar ba a bukatar ai mata wani dinke dinke mai yawa a jikinta.
Abubuwan da zaku tanada
Leda/fata
Tape
Almakashi
Yadda zaku hada.
Dafarko zaku dauki tape sai ku auna inchi 14 zuwa 16 fadi, tsayi kuma inchi 26 zuwa 28 (zaku iya karawako ku rage, wannan ya danganta da iya yadda kukeson girman jakar ta kasance.
  Saiku ninkata a kwance (yadda zurfin jakar zai bada inchi 13 zuwa 14) sannan saiku dauki tape ku fara aunawa daga kasan jakar ( inchi 3)  ta gefe guda, sai kuyi alama, sannan sai ku kuma auna inchi 3 a kwance daga dai kana jakar, sannan sai ku sa almakashi ku yanke yadda zai tashi kamar kwana. To yadda kukayi wannan haka zaku kuma maimaitawa a dayan gefenma. (nan wajen yanada dan wuyan fahimta ta hanyar bayani da baki shi yasa yanada kyau ku kalli videon nan dan ganin yada zakuyi cikin sauki https://youtu.be/X5tii-94p-M ku dannan link din ku gani.
  To bayan kun yanke kwanar guda biyu, saiku jiyu da jakar ta baibai ku dinko gefen jakar guda biyu, daga saman jakar har iya inda mukai wannan kwanar. Sannan sai ku kama wanan kwanar da mukai shima ku juyata a kwance yadda dinkin nan na gefen jakar zai tashi a tsakiya, sannan saiku dinkata........  Nan wajenma zaku fi fahimta in kuka kalli videon.
   To bayan anyi wannan shike nan sai ku juyo da jakar dai dai, in kunaso zaku iyayi mata kalmasa ta bakinta, anma ni banyiba. To sai a yanko hannayen jakar yanzu.
   In an tashi za ai hannu zaku iyayin mai tsayi ko guntu, ya danganta da yada kukeso, anma akalla zakusa daga misalin inchi 26 zuwa 36, fadin kuma sai ku sa inchi 1½  in bazakuyi kalmasa ba, anma in zakuyi shima zakusa akalla inchi 3.
  To bayan kun yanko wannan guda biyu. Saiku dinketa jikin jakar. Anma kafin ku dinke yanada kyau ku auna daga saman jakar zuwa daidai inda zaku manna dan kar wani yafi wani, hakama fadin gefen jakar. Duk wannan bayanin danai zaifi kyau ku hada da videon dan shine zai baku daman gani da kuma gane yadda zakuyi ku dinka kamar yadda na nuna. Ku danna link dinnan dan ganin videon https://youtu.be/X5tii-94p-M

Wednesday, 21 February 2018

YADDA ZAKU HADA TAKALMI MAI TUDU

Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa acigaba da kawo maku dabarun harhada abubuwa cikin sauki da kanku kuma acikin gidajenku. Ayau zan nuna maku yadda zaku hada takalmi mai tudu wanda akekira da kito ko wedges.
 
  Abubuwan da zaku tanada
Kwalin magwaji
Roba tik
Roba cushion
Almakashi
Yadi
Gam
Kibiya
Wuka
Yadda zaku hada
Dafarko in zaku hada wannan takalmi zaku samu wani takalmi wanda siffarsa tai yanayi da irin wannan da zamuyin. Sai ku daurashi a kan kwalin magwaji ku zana sannan kusa almakashi ku yanke.
   Bayan kunyi wannan saiku dauki wanan kwali ku daura akan roba tik kubida biro ku fidda suffar wannan takalmi (gaba daya kafar hagu da daman)
  Sai ku dakko roba cushion shima ku dora wannan kwali akansa ku zana sannan saiku yanke da almakashi. Anan zaku iya anfani da roba cushion kala 2 kamar yadda nayi, in kunaso zaku iyasa kala 3 koma 4. Sannan zaku iya sa hawa 2,3 ko 4 kamar yadda nayi. Abin lura kawai shine iya tudun da kukeso wannan takalmi ya baku iya hawa nawa zaku dora wannan roba cushion.
  Bayan kun fidda roba cushion dinda roba tik saiku dauki roba cushion wanda zai zama shine a saman takalminku ku auna inchi 2.7 daga sama wajen yatsu saiku sa kibiya ku huda, to anan zamusa igiyar takalmin. Saikuma mu koma can kasa wajan dunduniya mu auna inchi 3 sai mu yi alama ta gefe da gefen takalmin wato inda zamusa ragowar igiyoyin takalmin. Sai musa wuka mu tsaga dai dai fadin igiyar takalmin da zamuyi anfani dashi.
  To yanxu sai mu samu wani yadin wanda zamuyi igiyar takalmin dashi sai mu yanko kamar misalin inchi 6 da kuma wani misalin inchi 10 sai mu hadasu mu daure (ku duba link dinnan dan ganin yadda na daure nawa cikin video https://youtu.be/dEmWSO-qEY4)   To bayan kun daure saiku zura wannan igiyoyi cikin roba cushion din da kuka huda kamarbdai yadda na nuna acikin videon.
To yanzu sai mu dakko wannan roba tik mu shafa masa gam (gefen da ba zane) suma roba cushion din mu shafa gam, mu bari yasha iska kafin sai mu dakkosu mu jejjera yadda zai bamu hawa hawan da mukeso. Bayan mun jera sai mukai wajen masu gugan takakmi su gogo mana gefe gefen yadda zai tashi gaba daya kai daya. Shike nan mun gama takalminmu. Yanada kyau a kalli videon nan dan ganin yadda na fara hada takalmin da yadda ma ake goge takalmin , https://youtu.be/dEmWSO-qEY4 ku danna wannan link din kuga videon.

Tuesday, 20 February 2018

YADDA ZAKU HADA TAKALMI SILIFA



Assalamualaikum yan'uwa barka da warhakav ayau in sha Allah zamuyi bayanine akan yadda ake hada takalmi samfarin silifas.
Abubuwan sazaku tanada
Kwalin magwaji
Robar hancin takalmi
Roba tik
Roba sol
Igiya
Zamiya
Gam
Almakashi
Yadda zaku hada
Dafarko zaku samu kwalinku wanda zaku fidda surar takalmin dazaku hada, saiku sami wani takalmin wanda kukeso kasansa ya zama kamar wanda zakuyi, saiku dora akan kwalin nan sannan saiku bi ku zana da biro. Bayan kun zana saikusa almakashi ku yanke daidai kan biron.
Saiku dauki wannan kwalin da kuka yanko ku dora akan roba Tik ku kara tisawa da biro sannan saiku sa almakashi ku yanke. In kun tashi zaku fidda kafar dama da kafar hagu. Saiku kuma daukan wannan kwalin ku dora akan roba sol shima ku zana kafar dama da ta hagu.
  To yanzu sai ku dauki wannan roba sol din ku auna incin 2 ba waya(kafa) 2 sai kuyi alama da biru a daidai tsakiyar takalmin inda zai tashi sakanin yan yatsun kafa da kuma babbar yatsa ta kafa. Bayan nan sai ku dawo kasan takalmin wajen dunduniya shima ku auna inchi 3 sai kuyi alama, sannan sai ku dan kara gaba kadan ku karayin wata alamar ku kara matsawa gaba kadan kuyi wata alamar (alama 3 za ai saboda igiyoyin takalmin huda 3 zamusa a kowacce kafa)
Sai ku dakko igiyoyin takalmin ku auna inchi 8 guda biyu, inchi 14 guda 6, wannan igiyoyi dasu zamuyi anfani wajen yin igiyoyin takalmin.
( Anan ya kamata ku dakata ku kalli videon dankuga yadda na kitsa wannan igiyoyi suka bani wannan suffar da kuke gani, ga link nan ku danna zai sadaku da videon https://youtu.be/lsZ47HMuGe0)
Bayan kun kitsa wannan igiya sai ku kama Bakin ku sanya cikin wannan hudoji da mukai na takalmin.
  Sai ku samu san fefa ku goge jikin igiyoyin nan daidai inda zaku shafa gama sannan saiku fara kangawa ajikin kafarku dan ku san ko zaiyi maku cifcif ko akwai bukatar a rage ko a kara tsayin igiyoyin. (saboda wata kafar tafi wata tudu)
  To bayan anyi wannan sai a shafa gam a kasan roba sol da kuma roba tik din (inda baida zane) da kuma jikin zamiyar tagaba da baya, sai a jingine abarshi ya sha iska. Yadda za a gane ya sha iska shine in aka taba da hannu za aji baya danko sai a dakkosu asawannan zamiyar a tsakiyansu wato roba sol da tik din saina manne. To bayan anyi wannan sai asa guduma adan bubbuga sama sama yadda zasu manne sosai.
  To yanxu mun gama takalminmu sai kawai mu dauka mu kaiwa masu goge takalmi su gogo mana gabadaya zagayen takalmin yadda zai tashi kai daya. Wannan gugar batada tsada danmu nan suna goge mana akan naira 30. Kuma yawaici masu hada takalma ko gyaran takalma ne sukeyi. Duk wannan bayanin danai kuna iya kallonsa cikin video dan kufi fahimtar komai in sha Allah ,saiba danna wannan link din  https://youtu.be/lsZ47HMuGe0 dan ganin videon.

Monday, 19 February 2018

YADDA ZAKUYI TAKALMI MAI BEADS



Assalamu alaikum yan uwa, barkanmu da warhaka. Kamar kullum yauma mun taho maku da yadda zaku hada takalman nan masu beads cikin sauki kuma acikin gidajenku.
Abubuwan da zaku tanada
Beads
Allura
Zaren/ robar beads
Takalmi silifas
Sai gam
Yadda zaku hada
Dafarko zaku wari zare ko robar yin shiri wato nayin beads wadatacce sai ku sanya cikin allura. Sai ku dauki takalmin ku zura allurar ta saman takalmin daidai inda yake zama a tsakakkanin babban yatsar kafa da sauran yastun kafar. Saiku bullo dashi ta kasa sannan ku kuma tsirawa ku maido da allurar tabbullo sama kamar dai za ai dinki. (akwai video yanada kyau ku duba saboda ku kara fahimtar bayani na )
  Bayan kun ziro zaren sai ku ajiye takalmin a gefe, sannan ku sake yankan wani zaren ku kirga beads guda 6 sai kubzira acikin wannan zaren da kuka yanko, sai ku kama bakin zaren dayake hannunku na dama ku shigar dashi cikin beads din da yake hannunku na hagu.
Shikuma zaren da yake hannunku na hagu sai ku shigar dashi cikin beads din da yake hannunku na dama. In kukai haka zai baku round kamar fulawa. (https://youtu.be/3pybox7OyJs adanna link dan ganin abinda nake nufi)
  To haka zakuyi tayi har sai kunyi kamar guda 8 ko 6 sai ku dauki ko wani guda daya da kukayi ku rika dinkawa a jikin igiyar takalmin nan da zare da allura (anmafa zaren roba nayin shiri) idan kunaso zaku iyayi ajikin igiya daya kamar yadda nayi ko kuyi ajikin dukka igiyoyin guda biyu. Yanada kyau ku kalli videon shine zaisa ku fi fahimtar yadda zaku dinka beads din a jikin takalmin cikin sauki.
   To bayan kun dinka wannan sai ku dauki wani beads din (sosamu kusa wayanda suka fi na farkon girma) saiku rika diga gam wanda akesawa da bindiga sannan ku dora beads din akai. Kamar yadda nanuna acikin videon.
   To in a jikin igiya daya kukayi dinkin beads din nan masu fulawa, saiku dauki dayan beads din manya ku dinkasu suma ajikin sauran igiyoyin takalman. Adanna link din nan dan ganin bayanin yadda na fara sanya beads din har karshe https://youtu.be/3pybox7OyJs

Wednesday, 14 February 2018

YADDA ZAKU HADA MADAURIN KAI NA MATA (HEAD BAND)



Assalamualaikum barkanmu da warhaka, ayau in sha ALLAH zamuyi bayani akan yadda zaku dinka abin adon mata na kai wato head band, wannan zamu koyar da iri biyu ne anma kusan dayane saboda banbancinsu bamai yawa bane.

Abinda zaku tanada
Yadi mai roba
Zare da allura
Beads
Botir
 
Yadda zaku dinka (1)
Dafarko za'a auna ko inci nawa akeson tsayin wannan band din, wannan zan muku misali dana yara yan shekara 8-12,  in kuna so kuyi na manya saiku kara awon, in kuma na jarirai ne sai ku rage. Abi mafi sauki wajen sanin iya adadin daza asa shine a dauki tape a zagaya kan yarinyar da za aiwa sai asan nawa ne inchin da za asa.
To kamar yadda nai bayani wannan zamusa inci 20 tsyin fadin kuma inchi 9, sai a ninka a tsaye yadda zaibada 20by4½. Sai a dinke gefen yadda zai tashi dogo kamar safa anma bakin 2 abude.  Sai asa hannu a juyo dashi dai dai.
  Bayan anyi wannan saikuma akama bakin guda biyu asa zare da allura adinkesu (adanna link din nan dan ganin yadda za a dinke https://youtu.be/xax478NYRWI)
  To sai kuma a dakko Beads din shima ayi anfani da zare da allura a dinke adaidai saitin inda muka dinke din nan yadda zai zamana beads din sun rufe dinkin ba a ganin sa gaba daya (Ku danna link dan a kalli videon dan fahimtar abunda nake nufi anan https://youtu.be/xax478NYRWI)
Yadda za ku hada (2)
Wannan shima kamar wancen zaku auna ku yanka ku kuma dinke gefensa sannan ajuyo dashi dai dai.
To sai akama bakinsa guda 2 adinke da keke ko da zare da allura. Sai a yanko wani yadin kamar misalin inci 3 fadi da tsayinsa sai aninka shi 2 a dinke gefe daya sai shima asa hannu ajuyo dashi daidai sannan sai a daukeshi arufe wannan dinki da mukai na tsakiyan dashi. Shima a dinke nasa bakin https://youtu.be/xax478NYRWI Ku danna link din dankuga abinda nake nufi anan.
  To sai a dakko botir din, sai asa da gam ko da zare da allura agaban band din. Shikenan.
  Adanna link din akalli videon dan ganin irin yadin da botir din da nayi anfani da.
https://youtu.be/xax478NYRWI

Tuesday, 13 February 2018

YADDA ZAKU DINKA HULAR TURBÄN (2)

Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da warhaka. Ayau zamuyi bayani akan yadda zaku dinka turban a karo Na biyu, wannan hular yanayin dinkinta akwai banbanci dawacen da mukai na farko.

Abubuwan da za a tanada
Yadi mai karen miski
Tape
Almakashi
Zare da allura
Keken dinki.

Yadda za ayi
Dafarko za'a fara da auna tsayi da fadin yadin daza ai anfani dashi. A wannan zamuyi amfani Da inchi 40 A tsayin, fadin kuma inchi 12.
To bayan mun auna munsa almakashi muna yanki iya abuda zamu bukata to sai a ninka shi gida biyu a kwance (wato ya zama 20 by 12) sai a dinke gefe 3, dayan gefen shima za a dinke anma za abar fili misalin inci 2½ a farko da karshen wannan gefen (to nan baza a dinke ba)  yana da kyau akalli vidion dan ganin inda za a dinke din da kuma inda za a tsallake, ga link din https://youtu.be/IktQIe4qlAo a danna sai a kalli videon.
  To bayan an dinko sai a kama tsakiyar wannan yadi da muka dinko a tura gefe daya cikin daya gefen, yadda zai tashi kamar buhu, kuma wannan fili da muka bari bamu dinkeba (inchi 2½) zasu koma guri guda. Adanna link dan ganin abinda nake nufi anan https://youtu.be/IktQIe4qlAo
  To yanzu sai a kuma yanko wani yadin misalin inchi 7 fadi tsayi kuma inchi 8 sai a ninka a tsaye a dinke gefen sannan sai asa hannu a juyo dashi dai dai. Sai a dauki wannan hula da muka fara sai asa hannu ta cikin wannan huda a zuro wannan yadi mai inchi 7by 8 a hade bakinsa a dinke ta cikin hular. (wannan waje yanada kyau a tsaya a kalli videon dan afi fahimtar bayanina, ga link ku danna ku gani https://youtu.be/IktQIe4qlAo)
To da anyi wannan sai a jiyo bayan hular asa zare da allura ta daidai saman hular a yi tattara daga sama zuwa kasa ta wajen keyar k nan (anma za abar misalin 2½) sai atsaya anan atisa dinkin yadda bazai ware ba.
Da anyi wannan shi kenan za aga hular ta fito dai dai da irin wannan na jikin hotan, domin ganin yadda na dinka nawa daga farko har zuwa karshe saiku danna wannan link din https://youtu.be/IktQIe4qlAo.

Monday, 12 February 2018

YADDA ZAKU DINKA HULAR TURBÄN (1)

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa iri daban daban da kanku cikin gidajenku kuma acikin sauki. Ayau in sha Allah zan koya maku yadda zaku dinka hular turban ne, kuma zaku nimi wayannan abubuwa kamar haka.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi MAI karen miski (Velvet)
Tape
Almakashi
Zare da allura /keke
Fulawar ado (ba dole bane)

Yadda zaku dinka
Dafari zaku dauki tape sai ku auna yadin kamar haka (inchi 9 fadi, tsayi inci 11 ana yara)  (inchi 11 fadi, tsayi inchi 13 Na manya) to sai Ku sa almakashi ku yanka sannan ku ajiye Agefe.
Sai Ku kumasa tape ku auna inchi 3 fadi tsayi kuma inci 6 kusa almakashi ku yanka (wannan guda biyu zakuyi) in ba a gane bayaninaba ku danna link din nan dan ganin yadda na yanyanka komai daki daki https://youtu.be/5nxEuplsx08
Bayan kun yanyanka saikuma ku dauki wannan siraran da muka yanka ba karshe guda 2 Ku ninkasu a tsaye yadda zaibada inchi 1½ a maimakon inchi 3 sai kusa almakashi ta daidai bakin ku yanka a karkace sannan ku dinkesu yadda zaibaku kusurwa (yanada kyau a kalli video din nan dan ganin yadda nai. Ku dannan link dan ganin videon https://youtu.be/5nxEuplsx08)
  To yanzu sai ku dakko wannan yadi da muka fara yankawa (11 by 13) ku ninka shi a kwance yadda zai baku 11 by 6½ inchs. Sai ku dauki wannan siririn yadi da muka hada kusurwan dashi shima Ku ninka gida biyu sannan sai ku daidaitasu ku dinkesu atare yadda wannan kusurwa zata tashi a daidai tsakiyar wannan hula.
  Bayan an dinke sai a dawa ta bayan hular (wato wajen keyan) sai asa zare da allura a tattare gefe biyun anma a rage kamar misalin inci 4. https://youtu.be/5nxEuplsx08 Ku danna link din kuga abinda nake nufi in ba a fahimtaba.
  Yanzu sai a sa almakashi a yanko wani yadin mai fadi misalin inchi 20 tsayin kuma inchi 35 ko fi,  yadanganta da iya sau nawa akeso a zagayo da daurin aka in anzo daurawa. To sai a zuro dashi ta daidai inda muka rage inchi 4 dinnan sannan asa keke a dinke.
  Duk Wannan dinki in mutum baida keken dinki zai iya anfani da zare da allura wajen yinshi, sannan kuma yana da kyau a kalli videon da na hada da wannan rubutu dan afi fahimtar bayanin da nake.  https://youtu.be/5nxEuplsx08 ga link din videon sai a danna a kalli videon.
 

Wednesday, 7 February 2018

YADDA ZAKU DINKA TURO FILON SARAKAI

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da warhaka, ayau zamu koya maku yadda zaku dinka turofilo (throw Pillow) irin na sarauta.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi (mai karen miski)
Fiber dan duri
Botir 2
Tape
Zare da allura
Almakashi

Yadda zaku dinka
Dafarko zaku auna tsayi da fadin da kukeson filon ku ya kasance, wato in babba zakuyi ko karami, misali in kukasa tsayin yadin inchi 45 to fadin zakusa inchi 20 (in kunaso yayi tudu) anma in bakwasonsa da tudu saikusa inchi 17 amaimakon 20.
Bayan kun auna saikusa almakashi ku yanka sannan sai ku kama bakin yadin guda biyu ku ninka gida 2 (yadda zaibaku inchi 20 by 22½) idan ba'a fahimci bayaninaba a danna link dinnan https://youtu.be/3G2DJGIDiQo dan ganin abinda nake bayanin cikin hotan video)
  To bayan an ninka sai a hau keke a dinke gefe guda yadda zai tashi kamar siket, wato sama a bude kasama abude. Saikuma ku dauki zare da allura (ayi anfani da zare mai karfi kamar lilo/silo) sai ku kama saman yadin ku yi yar tattara (wato ku rika shiga kuna fita da zaren har ku zagayo inda kuka fara) in kun zagayo saiku zuge bakin ku dinke ruf yadda bazai rika budewa ba.
  To sai ku kuma Maimaita tattatar a daya bakin yadin, anma wannan karan bazaku zuge bakin kamar yadda mukai Afarko ba. Za a barshi yadda zamu iya dura fibet acikine.
  Bayan kunyi wannan zai tashi kamar buhu, saiku ibi fiber ku dura aciki iya yadda kukeso ku cikashi sannan sai ku kama zaren da allurar ku karasa tattare saman wannan bakin filo da mukeyi kamar dai yadda mukai na farko, shima a tsukeshi sosai a dinke yadda bazai budeba.
  Kuna yin wannan zakuga ya baku suffar wannan filo to anma bazamu bashi hakaba, sai kuma a dakko wayannan botirar asa ta saman pilon sannan a ziro da allurar ta tsakiyan filon ya bullo ta kasan sai a kuma sa dayan botir din akuma maimaitawa (yanada kyau adan matse hannu wajen wannan dinkin.
  Ku danna wannan link din dan ganin videon yadda na hada nawa filon https://youtu.be/3G2DJGIDiQo

YADDA ZAKU DINKA TURO FILON SARAKAI

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da warhaka, ayau zamu koya maku yadda zaku dinka turofilo (throw Pillow) irin na sarauta.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi (mai karen miski)
Fiber dan duri
Botir 2
Tape
Zare da allura
Almakashi

Yadda zaku dinka
Dafarko zaku auna tsayi da fadin da kukeson filon ku ya kasance, wato in babba zakuyi ko karami, misali in kukasa tsayin yadin inchi 45 to fadin zakusa inchi 20 (in kunaso yayi tudu) anma in bakwasonsa da tudu saikusa inchi 17 amaimakon 20.
Bayan kun auna saikusa almakashi ku yanka sannan sai ku kama bakin yadin guda biyu ku ninka gida 2 (yadda zaibaku inchi 20 by 22½) idan ba'a fahimci bayaninaba a danna link dinnan https://youtu.be/3G2DJGIDiQo dan ganin abinda nake bayanin cikin hotan video)
  To bayan an ninka sai a hau keke a dinke gefe guda yadda zai tashi kamar siket, wato sama a bude kasama abude. Saikuma ku dauki zare da allura (ayi anfani da zare mai karfi kamar lilo/silo) sai ku kama saman yadin ku yi yar tattara (wato ku rika shiga kuna fita da zaren har ku zagayo inda kuka fara) in kun zagayo saiku zuge bakin ku dinke ruf yadda bazai rika budewa ba.
  To sai ku kuma Maimaita tattatar a daya bakin yadin, anma wannan karan bazaku zuge bakin kamar yadda mukai Afarko ba. Za a barshi yadda zamu iya dura fibet acikine.
  Bayan kunyi wannan zai tashi kamar buhu, saiku ibi fiber ku dura aciki iya yadda kukeso ku cikashi sannan sai ku kama zaren da allurar ku karasa tattare saman wannan bakin filo da mukeyi kamar dai yadda mukai na farko, shima a tsukeshi sosai a dinke yadda bazai budeba.
  Kuna yin wannan zakuga ya baku suffar wannan filo to anma bazamu bashi hakaba, sai kuma a dakko wayannan botirar asa ta saman pilon sannan a ziro da allurar ta tsakiyan filon ya bullo ta kasan sai a kuma sa dayan botir din akuma maimaitawa (yanada kyau adan matse hannu wajen wannan dinkin.
  Ku danna wannan link din dan ganin videon yadda na hada nawa filon https://youtu.be/3G2DJGIDiQo

Tuesday, 6 February 2018

YADDA AKE DINKIN FILO MAI SUFFAR TATTASAI

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku yadda zaku rika harhada abubuwa da kanku cikin sauki. Ayau zan nuna maku yadda zaku dinka filo mai suffar tattasai.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi mai karen miski (Velvet)
Fiber dan duri
Zare da allura
Almakashi

Yadda zaku hada
Dafarko idan zakuyi wannan filo zaku shimfida yadinku a kasa sai ku ninka biyu anma a karkace yadda zai baku shape din kwarkwaro ko bututu (ku danna link dan ganin yadda zaku ninka https://youtu.be/oQcXNgPXYx8)
Bayan kun ninka saikuma kusa almakashi ku yanke ta saman iya tsayin da kuke so kuyi.
Saiku dauki wannan mai kamar kwarkwaron saiku ninka shi ta baibai sannan sai ku dinkeshi  a tsaye yadda zai tashi kamar dai yadda kwarkwaro yake (nayin kunshin fulawa)
To sai ku dakko zare da allura ku kama saman wannan kwarkwaro inda yake da fadi ku rika sa allurar ciki kuna fita kamar zakuyi tattara. Sai kuyi ta tatarewa har ku zagaye saman wannan kwarkwaron. To sai ku dakko fiber ku dura a ciki sannan saiku xuge bakin kwarkwaron (kuna zugewa zakuga ya baku suffar tattasai)
  To sai ku dakko wani yadin karami shima kuyi mar kamar yadda mukai Na farkon (wannan shine hancin tattasan, shima bayan an dinke za ai duri a zuge.
Yobisi kuma ku dauki kallar yadin da kukayi hancin tattasan ku fidda suffar ganye a jiki, in kunaso zaku iya mar duri shima ko kuma ku barshi hakannan.
  To yanzu saiku dakko tattasan ku sa hancin tattasan da kuma ganyen ku hadesu jikinsa a zare da allura. Yana da kyau ku kalli videon dan ganin yadda nayi wannan filon, domin ganin yadda na hada ku danna link dinnan https://youtu.be/oQcXNgPXYx8
Sai mun hadu a wani filon in sha ALLAH.

Monday, 5 February 2018

YADDA ZAKUYI PILLOW MARA DINKI

Assalamualaikum yan uwa, barkanmu da warhaka, Ayau darasinmu zamuyi akan throw Pillow ne wanda in za ayi ba'a bukatar gam, zare da allura ko keken dinki wajen hadashi.

abubuwan da za a tanada
Yadi mai tsantsi (satin)
Pillow mai kwana 4

Yadda ake hadawa
Da farko za a tanadi pilow wanda yake mai kwana 4, in ba ada pillo sai a dinka daya, saboda wannan wanda zamuyi zai zama kamar gidan pilo ne zamuyiwa pilon.
To sai a dakko yadin a shimfida a kasa,  yadin ya zamana duk gefen hudun kansu daya, misali in inchi 20 ne saman to kasan ma haka za asa gefe da gefenma haka za asa.
Sai a dakko pilon asa a tsakiya anma akarkace (aduba wannan Link din dan ganin hotan yadda za asa pillon https://youtu.be/sjf2U6VphXc)
Bayan ansa sai a kama leben yadin guda biyu a lankwasosu a tura kasan wannan pilon,  ku duba videon dan ganin yada ake turawar dan bazai bayanu da baki ba) bayan anyi wannan sai kuma a dakko dayan bakin yadin guda 2 sai a kama a daure (kamar yadda ake daure abincin sallah acikin dankwali muna yara 😀)
In an daure sai kuma a gyara gun da aka daure. In anaso sai abarshi haka in kuma anaso sai asamu wani yadin (ni nasa ruwan hoda)  sai shima a daure akan wancan kullin da akai na farko.  Sannan sai a juya kullin yadda kullin zai koma ciki.
Wannan shine yadda ake yin wannan pilon, yanada kyau a kalli videon dan ganin yadda na hada komai cikin sauki, ku danna link dan gannin videon https://youtu.be/sjf2U6VphXc.
In an tashi za a wanke pillon saidai kawai a kwance daurin a wanke in ya bushe a goge a kuma daurewa.

Wednesday, 31 January 2018

YADDA ZAKU HADA TUKUNYAR FULAWA

Assalamualaikum, yan uwa barkanmu da warhaka, barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku hanyoyi da dabaru na hada abubuwa daban daban cikin sauki acikin gidajenmu.
  A yau zan nuna maku yadda zaku sarrafa tsofaffin takardu da jaridu wajen hada tukunyar fulawa a maimakon zubarwa da mukeyi abaya.

Abubuwan da zaku tanada
Takardu /jaridu
Farin gam (top bond)
Tishu (tissue p)
Balo (ballon)
Almakashi
Brushi
Fenti
Kofi

Yadda ake hadawa
Afarko za asamu jaridunne a sa almakashi a yanyanka kanana sai a ajiye a gefe.
Sai kuma a dakko balo din a hura da an girma sai a daure bakin a dorashi akan kicin (wajen kullin a kasa) ku zuba link din DAN ganin abinda nake nufi anan. https://youtu.be/4BXbvsrhP0o
Sai ku dakko wannan gam din kurika shafawa da burushin ajikin balo din, bayan kun shashshafa  saiku dauki Takardun nan kubi duk jikin balo din ku Manna, saiku kara shafa gam din akan takardan ku kara bi da takardun ku manne (ku danna link din videon dan ganin abinda nake nufi anan https://youtu.be/4BXbvsrhP0o)
Bayan anyi wannan akalla hawa 5 saikuma a dakko tissue din shima ayi masa kamar yadda akaiwa takardannan. Saina ajiye a gefe abarshi ya kwana saboda ya bushe baki daya.
Bayan ya bushe sai a dakko almakashi a yanke bakin balo din sai kuma akuma sa almakashi a gyara saman wannan tukunya da aka hada. Sannan a shafe/fesheshi  shi da fenti, in ya bushe sai a dakko fulawar asa aciki.
Wannan shine yadda zaku Hada tukunyar fulawarku da takardu cikin sauki, duk inda ba a fahimci bayanin da naiba to ayi kokari a kalli videon yadda na hada saboda asamu saukin fahimta, a danna wannan link  https://youtu.be/4BXbvsrhP0odin dan ganin videon.

Tuesday, 30 January 2018

YADDA ZAKU HADA ABUN KWALLIYAR BANGO

Assalamualaikum yan uwa. Ayau ma zamuyi bayani akan yadda zamu hada kayan adon bango wato kayan decoration Na gidajenmu cikin sauki.
   Sana'ar decoration sana'ace mai matukar farin jini acikin al'unmam mu a wannan lokaci, sabanin abaya,  dayawan mata sun gane sirrin dake cikin gyara tare da kawata gidajensu ta hanyar decoration, wannan yasa a wannan satin bayananmu zasu raba'a akan yadda zamubi mu gyara gidajenmu sannan alokaci guda ku rike wannan harka a matsayin sana'a dan cigabanmu.

Abubuwan da za a tanada

Straw (tsinken lemo)
Spray paint (penti)
Hot glue (gam)
Kwali
Flower
Ribbon/bayis

Yadda zaku hada

Dafarko za a dauki kwalin sai ayankashi yadda zai bada sufar rawun (round) idan an yankashi sai a samu biro a zana wani rawun/circle a tsakiyar wannan kwalin.
  Bayan anyi wannan sai a dakko straw din a rika shafa gam din ajiki daga baki bakin sa ana likawa jikin kwalin ta dai dai kan wannan biro da muka zana a tsakiyan kwalin, haka zakuyi ta manna straw din har sai kun zagaye gaba daya jikin wannan kwalin.
  To bayan kun jejjera sai kuma ku dakko flowers dinku saiku rika sa gam kuna jejjerawa a saman kwalin DAN ganin yadda zaku hada flowers (FULAWA)din ku danna link dinnan https://youtu.be/Hfq3cI9Ju3w
  Bayan kun gama jerawa sai kuma ku dakko pentinku ku feshe gaba daya wannan abun decoration da kukayi. Bayan wannan saiku dauki bayis ko Ribbon ku manna bayan kwalin yadda zaku rika ratayewa jikin bango.
  Wannan shine yadda zaku hada wannan abun decoration cikin sauki, dan ganin yadda na hada da kuma kayan aikin danai anfani da saiku duba wannan videon https://youtu.be/XNVLzjOEQdc

Monday, 29 January 2018

YADDA ZAKU HADA ABUN ADON BANGO

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da war haka, sannunmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa da Sana'oin hannu a gidajenku kuma cikin sauki.
Ayau zan koya maku yadda zaku hada abin adon bango wato wall hangings/ decor. wannan abun kwalliyar daki yanada matukar kawatawa kuma ana hada shi cikin sauki ba tareda an kashe kudi dayawa ba. Batare da bata lokaciba zaku bukaci abubuwan aiki kamar su.....

Abubuwan da zaku tanada

Cokula Na roba
Madubi (round)
Kwali
Penti (spray paint)
Faranti (circle)
Kyalli (glitters)
Almakashi
Gam (glue gun /stick)
Ribbon (ko bayis)

Yadda zaku hada

Dafarko idan zakuyi wannan abun adon bango zaku nimi cokula na roba sai kusa almakashi ku ciccire kan cokalin https://youtu.be/M1SAEbhAEec. Shi kuma ainihin marikin cokalin sai ku adana (badashi zamuyi anfaniba yau)
Sai Ku dakko kwalinku saiku ajiye akasa sannan saiku dakko faranti ku daura akai kubi jikin farantin da biru (tracing) in kin zana kusa almakashi ku yanka.
Sai Ku dauki wannan kwali da kuka yanka mai zagaye ku ajiye akasa sannan ku dakko madubinku ku daura akai, a daidai tsakiyar (ku tabbata mudubin baikai girman kwalinba) kina iya danna link dinnan dan ganin abinda nake nufi https://youtu.be/M1SAEbhAEec.
Bayan kun sa mudubin kun zana (tracing) a wannan karan bazaku sa almakashi ku yanka ba, sai Ku rika dakko wannan kan cokula da kuka yanyanke ku rika sa gam ta bayan cokalin sannan sai ku rika mannawa ajikin wannan kwalin(zaku fara daga daidai kan layin da kukaja na tsakiyar kwalin) wato dai dai inda zakusa madubin.
  Haka zakuyi ta sa gam ajikin cokalin kuna mannawa har sai kun cike duka jikin kwalin sannan sai ku dakko penti ku shafe jikin wannan cokula dashi(har bayan kwalin)
Kafin ku fara fesa pentin yanada kyau ku shin fida kwali akasa saboda karya bata maku waje) bayan kun fesa pentin saikuma ku dakko kyalli ku yaryada akan wannan fenti da sauri kafin ya fara bushewa. Kuna sawa saiku sa gam a daidai tsakiyar kwalin sannan saiku daura mudubin, ku sa hannu kudan danna yadda zai kame.
  Bayan kunyi wannan saiku juyo bayan kwalin ku dakko wannan ribbon ko bayis din ku sa gam ku manna da jikin kwalin yadda zai kame ajikin kwalin, to wannan dashi zaku manna abun adon bangon ajikin bango.
Wannan shine yadda zaku hada naku decoration din cikin sauki. Domin karin bayani kuna iya danna wannan link din https://youtu.be/M1SAEbhAEec dan ganin yadda na fara hada wannan abun decoration tundaga farko har karshe. Hakan zai kara baku daman fahimtar komai cikin sauki in sha ALLAH, shi yasa na dauki hoton komai cikin video yadda Za'aga komai. To sai mun hadu a wani darasin.

Wednesday, 24 January 2018

YADDA ZAKU HADA MAN LEBE (LIP BALM)

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku darussa akan yadda zaku rika hada abubuwa daban daban da kanku cikin sauki, ayau zan nuna maku yadda zaku hada man lebe da kuma man da zai sanya labbanku taushi da tsantsi in sha ALLAH.

1) lip moisturiser
Abubuwan da zaku tanada

Vaseline ½ cokali
Man kade ½ cokali
Zuma ¼ cokali
Hand dryer
Kwanu
Mazubi

Yadda zaku hada

Dafarko zaku dauki kwanu (bowl)sai ku ibi wannan Vaseline din da man kade ku sanya cikin kwanun saiku dauko hand dryer wato abun busar da gashi, saiku kunna wajen dumin saikuyi anfani dashi wajen narka wannan mai. 
Bayan ya narke saiku dakko zuma saiku sa a ciki sannan saiku jujjuya, saiku samu mazubi mai kyau saiku juye aciki. Saiku ajiye kubarshi da ya huce zai kame jikansa.
Wannan  mai in kuna shafawa  lebenku zai kasance da laushi kuma ya hana bushewa da tsagewa. Dan ganin yadda nai nawa man ku danna link dinnan https://youtu.be/CjfXtbyS4XU . bayan wannan kuma sai dayan man da zan nuna maku kamar haka

2) lip balm
Abubuwan da zaku tanada

Vaseline ½
Man kade ½
Jan baki (kowane kala)
Mazubi
Sai kwanun da za a hada aciki

Yadda zaku hada

Shima wannan kamar wancen wanda mukai ne na farko, zaku dauki Vaseline da man kade ku juye a kwanu saiku sa abin busar da gashi ku narka, idan mutum baida abun busar da gashi zai iya sawa ciki microwave ko ayi anfani da double boiler kamar yadda mukai lokacin da mukayi man gyaran jiki da gashi.
To bayan an narka saikuma a dakko jambaki a gutsiri kadan asa acikin man sai ajuya harsai shima ya narke gaba daya. In anada ragowar jambaki irin wanda ya riga ya kare sai kawai asa abu a dan kwakulo cikin jambakin ayi anfani dashi.
Inya narke sai a juye a robar mai mai kyau abarshi ya daskare a hankali. DAN ganin yadda Nai nawa man saiku Danna link dinnan dan ganin videon https://youtu.be/CjfXtbyS4XU
Wannan shine yadda zaku hada man lebe cikin sauki kuma ya sanya maku taushi da tsantsi a koda yaushe.

YADDA ZAKU HADA MAGANIN GYARAN NONO

Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa daban daban cikin sauki kuma a cikin gidajenmu. Ayau zamuyi magana ne akan gyaran jiki musanmam gyaran nono, ga mai sha'wa ta gyara jikinta ko ta fara hada na sayarwa zata bi wannan hanyar wajen cimma nasarar gyara cikin sauki.

Abubuwan daza a tanada

Garin hulba gwangwani 1
Garin si'itir gwangwani 1
Alkama gwangwani 2
Gyada gwangwani 2

Yadda zaku hada

Dafarko za a fara gyara alkama da gyada a wanke a shanya su bushe sosai sannan sai akai nika a niko su, bayan an niko sai a samu leda mai kyau mai fadi ko faranti babba a bajesu ashanya su sake bushewa sosai.
Sannan sai a samu rariya a tankade a fidda dusan. Shi kuma garin mai laushi sai a samu roba mai kyau sai ajuye aciki.
Saikuma adakko garin hulba da si'itir din shima a hadesu cikin wani roba mai kyau a jiye.

Yadda ake anfani dashi.

Hadin alkama da gyada cokali 2
Hadin hulba da si'itir ½ cokali
Ruwa misalin kopi 1½

Idan aka tashi za ai anfani dashi za a samu ruwa da dan yawa (misali in anaso ayi anfani da ruwa kopi 1ne to sai asa kopi 1½) akan wuta, a dauki cokali a ibi garin hulban da si'itir din nan misalin ½ cokali (ba a'sawa dayawa) sai azuba cikin ruwannan abari ya tafaso.
Agefe guda kuma sai a ibi garin alkamar nan da gyada misalin cokali 2 a danyi kamar za ai talge in ruwan da muka daura a wuta ya tafaso sai a juye wannan kullin da muka dama ai talge dashi (ba'aso yayi kauri) saboda xamu barshi akan wuta saiya dahu, anma fa arikayi ana juyawa saboda karya kama.
In an tabbatar ya dahu sai a juye asamu madara da dan suga asa, sai asha Da dumi. Za a iyayin wannan kullum sau daya, in sha Allah bayan sati 2  ajere za a fara jin/ganin canji.

Monday, 22 January 2018

YADDA ZAKU HADA SHAMPOO A GIDA

Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa da Sana'oin hannu cikin sauki. Ayau munxo maku da yadda zaku hada shampoo da kanku cikin sauki, dan sannin yadda zaku hada shampoo to ku kasance tare da damu.

Abubuwan bukata

Ruwa liter 1
Antisol cokali 3
Sls cokali 1
Caustic soda cokali 1
Soda ash cokali 1
Sulphuric acid cokali 1½
Texapone cokali 3
Methanol ½ cokali
Kala (daidai misali)
Turare
Glycerine cokali 1
Vitamin E cokali 1

Yadda zaku hada

Dafarko zaku samu antisole  sai ku samu robar da zaku hada shampoo din aciki ku zuba sanna ku zuba ruwa ku barshi yayi misalin awa 24, in kunaso ma zaku iya barinshi ya kwana 2.
Bayan ya jiku saiku dakko sls din ku juye akai, sannan sai kusa abu ku jujjuya har sai kunga ya hade.
Daga nan saikuma ku dakko Caustic soda sai ku zuba akai, ku cigaba da juyawa harsai kunga ya hade sosai. In kinaso zaku iya jkawa da ruwa kadan kafin ku hadesu.
Saikuma ku dakko soda ash shima ku juye aciki. Shima aita juyawa harya narke.
Saikuma adakko Sulphuric acid shima azuba. Aita juyawa Sosai. Bayan ansa wannan sai a dakko texapone shima ajuye ayi ta juyawa harsai ya hade jikinsa sosai.
To sai kuma ku dakko methanol shima kusa, kucigaba da juyawa inya hade saiku dakko kala (duk wacce kukeso kusa) to saiku jujjuya har sai ya hade gaba daya.
To sai kuma ku dakko turare kusa, ku dako glycerine da vitamin E kusa ku jujjuya shike nan.
Wannan shine yadda ake hada shampoo a gida, DAN ganin yadda na hada nawa saiku danna wannan link din
https://youtu.be/2Qq5Krslk60 dan ganin videon yadda na hada shampoo na daga farko har karshe. To sai mun hadu a wani darasin.

Wednesday, 17 January 2018

YADDA ZAKU HADA AIRFREASHNER A GIDA

Assalamualaikum yan'uwa, barkanmu da sake saduwa a cigaba da kawo maku darussa akan yadda zaku rika hada abubuwa daban daban da kanku a cikin gidajenku, a yau Zan nuna maku yadda zaku hada airfreashner ne Wato turaren daki cikin sauki.

Abubuwan da za'a tanada
Ruwa liter 1
Texapon cokali 3
Methanol Rabin Rabin liter
Turare (lavender)
Kala
Mazubi

Yadda zaku hada
Datar zaku samu roba mai fadi, Wanda za mu hada komai aciki, sai a dakko texapone a sa aciki sannan a dakko Wannan methanol din a juye akai, sai asa abu a jujjuya har sai ya hade gaba daya.
Sai kuma a dakko ruwan sai a juye akai, shima a jujjuya, bayan an juya ya hadu sai a dakko kalar da akeso ayi anfani da, ni nayi anfani da ruwan hodane, sai  a sa a wani robar a sa ruwa kadan yadda zai narke kafi a juye a Cikin wanan hadin turare da mukeyi.
Bayan an juye sai kuma a dakko turaren (zaku iya sa Wanda kuke so shima) bayan kunsa sai Ki jujjuya Sosai sannan sai ku samu mazubi irin na turare Ku juye aciki, Shike nan.
  Ga Wayanda suke da sha'awar suga yadda na hada nawa turaren Ku danna wannan link din Dan ganin videon https://youtu.be/LOSMy8fy2cs
Nagode.

Tuesday, 16 January 2018

YADDA ZAKU HADA SABULUN WANKE WANKE (LIQUID SOAP)

Assalamualaikum yan uwa matasa, a yau zamu koya maku yadda ake hada sabulun wanke wanke Wanda aka fi Kira da liquid soap.

Abubuwan da za'a tanada
Nitrosol
Caustic soda
Soda ash
Sulphuric acid
Texapon
Kala
Turare
Ruwa lita daya
Mazubi

Yadda ake hadawa
Dafarko Idan za ai Wannan sabulun, za asamu roba mai fadi, sai a dauki cokali a auna nitrosol cokali 2 a zuba acikin wannan robar mai fadin,  sai a dauki wannan ruwan a rabashi gida 2,azuba Rabin acikin nitrosol din Rabin kuma sai a ajiye a Gefe. Sai a samu wani abu a rika jujjuya wannan nitrosol da muka zuba ruwa a ciki har sai ya narke.
Sai kuma a samu wata robar karama a ibi ruwa daga cikin Wannan ragowar da muka ajiye, sai a zuba acikin wannan karamar roba sannan a ibi  caustic soda Rabin chokali azuba aciki, sai aita juyawa har sai ya narke. Sannan sai a juye a cikin Wannan roba mai fadi Wanda muka sa nitrosol a ciki, sai kuma Acigaba da juyawa.
Bayan sun hade sai kuma a ibi soda ash cokali 2 a zuba a Wannan karamar roba, a ibi ruwa kadan daga cikin Wannan Wanda muka rage a zuba akan soda ash din asa abu ajuya. In ya narke sai shima a juye akan nitrosol din nan na cikin robar nan mai fadi. Sai Acigaba da juyawa.
To sai a dakko sulphuric acid a ibi cokali 2, a zuba acikin wannan robar mai fadi na nitrosol Acigaba da juyawa.
Sai kuma a dakko texapone a ibi cokali 2 a asa a Wannan karamar roba sannan sai azuba wannan hadin nitrosol din akai, ana juyawa (za aga yana kauri) to sai arika karawa kadan kadan ana juyawa, in Kaurin ya daidaita sai a juyeshi acikin robar nitrosol din Acigaba da juyawa. Har sai anga gaba daya ya Hade waje guda.
To sai kuma a dakko kala, asa iya adadin da akeso acikin wannan karamar robar sai kuma ajuye ragowar ruwan munnan akai, ajuya Sosai sannan sai ajuye akan Wannan hadin nitrosol din, ajujjuya sannan daga karshe sai asa turare,  shima za'asa dai dai yadda ake so, sai ayita juyawa har ya hade gaba daya.
To in ya hadu Sosai Sai a samu mazubi mai kyau sai ajuye. Wannan shine yadda zaku hada sabulun wanke wanke (liquid soap) agida,  ga masu sha'awan suga yadda na hada nawa sabulun sai su danna wannan link din Dan ganin cikakken videon https://youtu.be/g-aNZRkiDxg

Monday, 15 January 2018

YADDA ZAKU HADA MAN GYARAN JIKI DA GASHI LOKACIN HUNTURU

Assalamualaikum yan uwa, a yau Zamu koya maku yadda ake hada man Gyaran jiki da kuma Gyaran Gashi musammam a Wannan yanayin da muke ciki na hunturu.
Wannan mai da Zamuyi bayaninshi a yau yanada saukin hadawa kuma yana gyara fata tai laushi da tsantsi sannan ya Hana fata bushewa da tsatstsagewa a yayin SANYI.

Abubuwan da za'a tanada
Man kwakwa
Man kade
Man habba
Zaitun lauz
Hand mixer
Mazubi.

Yadda ake hadawa
Da farko za asamu wani kwanu sai a zuba man Habba, zaitun lauz, man kwakwa da kuma man kade (Idan an tashi za asa man kade kopi daya, to man kwakwa Rabi za'asa, sauran man kuma sai asa rabi rabin kofi) bayan an hadesu a waje daya sai a samu tukunya a zuba ruwa a ciki kar yakai Rabin tukunyar, sai a Dora akan wuta sannan sai a dakko Wannan kwanun da mukasa sauran mayukanmu a ciki asa cikin Wannan tukunyar. Sannan sai a sa cokali a rika juyawa a hankali a hankali har sai man ya narke. Akula, in za a narka wannan man ba a dorawa akan wuta Kai tsaye inba hakaba za a kashe sinadaren da suke cikin man. Shi yasa ake bin wannan hanyar wajen narkawa.
  Bayan ya narke gaba daya sun hade sai asamu leda a rufe saman kwanun sannan asa a firinji a barshi sai ya Fara daskarewa (zai yi Kamar Kakide) sannan sai a dakko shi a sa mixer a rika gaurayawa Dashi harsai yayi laushi, za aga yayi Kamar kumfa kumfa, Idan mutum baida hand mixer to zai iya sa abin kada kwai irin mai karfinnan yayi ta kadawa Dashi har sai ya hade jikinsa.
Bayan ya hade Sosai sai a juye a wani mazubi mai kyau a rufe. Wannan man kowa zai iya anfani da shi babba da Yaro.

Wannan man yanada matukar anfani wajen Gyaran fata, domin yanasa fata tai laushi, yana cire narkanwa, yana maganin waskanai, yana Hana bushewar fata, yana maganin fashewar lebe, yasa fata sheki da kyau matuka. Sannan yana gyara Gashi yasa tsayi, Baki, laushi da cikowar suma.

Gamai shaawar taga yadda nayi na hada wannan mai tare da adadin danai anfani da sai Ki danna Wannan link din.....  https://youtu.be/3mBJW4V4zkI

Nagode, sai mun hadu a wani darasin.

Wednesday, 10 January 2018

YADDA AKEYIN MAN KWAKWA (2)

Abaya munyi bayanin akwai hanyoyin yin man kwakwa daban daban har mun koyar da yadda ake bin hanya ta farko wajen yin man kwakwa a gida,  ayau kuma zamu koya maku daya hanyar in sha Allah.

ABUBUWAN bukata:

Kwakwa
Ruwa
Wuka
Abin kankara
Abin markade
Tukunya
Yadi ko rariya
Mazubi.

Yadda akeyi:
Dafarko in za Ai man kwakwa za a Fara bare bawon kwakwarne, sannan sai a wanke kuma kankare wannan DAN jajajan jikin kwakwar,  bayan an kankare sai adau wuka a yanyanka ta kanana.
Bayan an yanmata sai a zuba a abin markade a zuba ruwa wadatacce sannan sai a markada har sai ya yi laushi.  Sannan sai a dakko yadin Tatar koko ko rariya mai laushi a tace wannan markade, sannan sai a juye ruwan kwakwar a wani mazubi mai fadi a saka cikin gidan firinji.
Idan za asa ba a sawa a gidan kankara, saboda banason ya kankare, za a barshi ciki harsai anga ruwan ya rabe 2, Wato ruwan kwakwar yai kasa man kwakwar tai sama.
Sai a dakko a yade wannan man kwakwar data kwanta a sama sannan sai a sa cikin tukunya a Dora akan wuta. Sai a rika juyawa LOKACI LOKACI har sai anga ya Fara curewa, kula za aga mai ta Fara tsatstsafowa, sai a rage wuta acikagaba da juyawa harsai wannan tika tika ta cure duka,  sai a sauke abarshi yasha iska, sannan sai a tace a juye a mazubi  Shike nan.

Dan ganin yadda na yi nawa man kwakwar daga farko har karshe ku danna wannan link din https://youtu.be/hFyKsPh5Qrg ko Ki danna hoton man kwakwar.

YADDA AKE YIN MANKWAKWA

Assalamualaikum yan'uwa,  ayau zamu koya maku yadda ake yin MANKWAKWA a gida.
Idan za Ai man kwakwa ana iya bin hanyoyin da dama wajen fidda man daga jikin kwakwa,  anma ayau Zamuyi muku bayani akan yadda ake yinsa ta hanyoyin biyu in sha Allah.

hanaya ta farko (1)

Abun da zaku tanada:
Farin kwakwa
Wuka
Ruwa
Abin markade (blender)
Yadi ko rariya
Tukunya
Mazubi

Yadda ake yi:
Da farko zaku sami farin kwakwa, saina bare bawon sannan sai a yanyanka kanana yadda zai mana dadin markadawa.
Bayan mun yanka sai mu wanke sannan sai asa a abin markade a zuba ruwa wadatacce a markada sai yayi laushi.
Bayan an markada sai adau rariya mai laushi ko yadi irin na Tatar koko sai a tace wannan ruwan kwakwa da muka markada.dusar kuma in Anaso za a iyayin kwakumeti ko biskit Dashi.
Shi kuma wannan ruwan kwakwa sai a juye a tukunya a Dora akan wuta a barshi yayita tafasa (Anma kar a rufe tukunyar). Haka za a barshi harsai ruwan ya Kare gaba daya za a GA mai ya Fara fita, Sai a rage wutar a hankali za aga gaba daya ruwan ya kone.
Sai a kashe wutar abari ya huce sannan sai a dau rariya ko wani yadi mai kyau sai a tace. Sai a dau man da aka tace asa ajuye a mazubi, dattin da aka tace kuma sai a zubar.

Tuesday, 9 January 2018

RAHHAJ'S HOME MADE INSPIRATIONS

Assalamualaikum yan uwa mata da maza, Rahhaj's na farincikin Sanar maku da cewar sun bude sabon channel dinsu a YouTube inda suke koyarda sana'oin hannu iri daban daban, Kama daga Dinkin kayan sawa, zannuwan gado, labulaye, takalma, jakunkuna, yari da sarka, dinkunan yar kanti ta yara, hada kayan kwalliyar gida Kamar kayan adon bango, kayan ado na daki, bandaki da kayan afani na jarirai.
     Bayan wayannan zamu rika koyarda kayan Gyaran jiki Kamarsu man shafawa, sabulai, turaruka, da wasu abubuwan da dama,  kudai Ku kasance damu Dan cin moriyar Wannan Garabasar.
   Domin kasancewa damu a channel dinmu na YouTube (rahhaj's home made inspirations) ku biyo Wannan link din
>>> https://www.youtube.com/channel/UCrl5ZMZofMdca6cHvwmT2_A

YADDA AKE HADA MAN KITSO

https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs