Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da warhaka. Ayau zamuyi bayani akan yadda zaku dinka turban a karo Na biyu, wannan hular yanayin dinkinta akwai banbanci dawacen da mukai na farko.
Abubuwan da za a tanada
Yadi mai karen miski
Tape
Almakashi
Zare da allura
Keken dinki.
Yadda za ayi
Dafarko za'a fara da auna tsayi da fadin yadin daza ai anfani dashi. A wannan zamuyi amfani Da inchi 40 A tsayin, fadin kuma inchi 12.
To bayan mun auna munsa almakashi muna yanki iya abuda zamu bukata to sai a ninka shi gida biyu a kwance (wato ya zama 20 by 12) sai a dinke gefe 3, dayan gefen shima za a dinke anma za abar fili misalin inci 2½ a farko da karshen wannan gefen (to nan baza a dinke ba) yana da kyau akalli vidion dan ganin inda za a dinke din da kuma inda za a tsallake, ga link din https://youtu.be/IktQIe4qlAo a danna sai a kalli videon.
To bayan an dinko sai a kama tsakiyar wannan yadi da muka dinko a tura gefe daya cikin daya gefen, yadda zai tashi kamar buhu, kuma wannan fili da muka bari bamu dinkeba (inchi 2½) zasu koma guri guda. Adanna link dan ganin abinda nake nufi anan https://youtu.be/IktQIe4qlAo
To yanzu sai a kuma yanko wani yadin misalin inchi 7 fadi tsayi kuma inchi 8 sai a ninka a tsaye a dinke gefen sannan sai asa hannu a juyo dashi dai dai. Sai a dauki wannan hula da muka fara sai asa hannu ta cikin wannan huda a zuro wannan yadi mai inchi 7by 8 a hade bakinsa a dinke ta cikin hular. (wannan waje yanada kyau a tsaya a kalli videon dan afi fahimtar bayanina, ga link ku danna ku gani https://youtu.be/IktQIe4qlAo)
To da anyi wannan sai a jiyo bayan hular asa zare da allura ta daidai saman hular a yi tattara daga sama zuwa kasa ta wajen keyar k nan (anma za abar misalin 2½) sai atsaya anan atisa dinkin yadda bazai ware ba.
Da anyi wannan shi kenan za aga hular ta fito dai dai da irin wannan na jikin hotan, domin ganin yadda na dinka nawa daga farko har zuwa karshe saiku danna wannan link din https://youtu.be/IktQIe4qlAo.
No comments:
Post a Comment