Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa acigaba da kawo maku dabarun harhada abubuwa cikin sauki da kanku kuma acikin gidajenku. Ayau zan nuna maku yadda zaku hada takalmi mai tudu wanda akekira da kito ko wedges.
Abubuwan da zaku tanada
Kwalin magwaji
Roba tik
Roba cushion
Almakashi
Yadi
Gam
Kibiya
Wuka
Kwalin magwaji
Roba tik
Roba cushion
Almakashi
Yadi
Gam
Kibiya
Wuka
Yadda zaku hada
Dafarko in zaku hada wannan takalmi zaku samu wani takalmi wanda siffarsa tai yanayi da irin wannan da zamuyin. Sai ku daurashi a kan kwalin magwaji ku zana sannan kusa almakashi ku yanke.
Bayan kunyi wannan saiku dauki wanan kwali ku daura akan roba tik kubida biro ku fidda suffar wannan takalmi (gaba daya kafar hagu da daman)
Sai ku dakko roba cushion shima ku dora wannan kwali akansa ku zana sannan saiku yanke da almakashi. Anan zaku iya anfani da roba cushion kala 2 kamar yadda nayi, in kunaso zaku iyasa kala 3 koma 4. Sannan zaku iya sa hawa 2,3 ko 4 kamar yadda nayi. Abin lura kawai shine iya tudun da kukeso wannan takalmi ya baku iya hawa nawa zaku dora wannan roba cushion.
Bayan kun fidda roba cushion dinda roba tik saiku dauki roba cushion wanda zai zama shine a saman takalminku ku auna inchi 2.7 daga sama wajen yatsu saiku sa kibiya ku huda, to anan zamusa igiyar takalmin. Saikuma mu koma can kasa wajan dunduniya mu auna inchi 3 sai mu yi alama ta gefe da gefen takalmin wato inda zamusa ragowar igiyoyin takalmin. Sai musa wuka mu tsaga dai dai fadin igiyar takalmin da zamuyi anfani dashi.
To yanxu sai mu samu wani yadin wanda zamuyi igiyar takalmin dashi sai mu yanko kamar misalin inchi 6 da kuma wani misalin inchi 10 sai mu hadasu mu daure (ku duba link dinnan dan ganin yadda na daure nawa cikin video https://youtu.be/dEmWSO-qEY4) To bayan kun daure saiku zura wannan igiyoyi cikin roba cushion din da kuka huda kamarbdai yadda na nuna acikin videon.
To yanzu sai mu dakko wannan roba tik mu shafa masa gam (gefen da ba zane) suma roba cushion din mu shafa gam, mu bari yasha iska kafin sai mu dakkosu mu jejjera yadda zai bamu hawa hawan da mukeso. Bayan mun jera sai mukai wajen masu gugan takakmi su gogo mana gefe gefen yadda zai tashi gaba daya kai daya. Shike nan mun gama takalminmu. Yanada kyau a kalli videon nan dan ganin yadda na fara hada takalmin da yadda ma ake goge takalmin , https://youtu.be/dEmWSO-qEY4 ku danna wannan link din kuga videon.

No comments:
Post a Comment