Assalamualaikum yan'uwa barka da warhakav ayau in sha Allah zamuyi bayanine akan yadda ake hada takalmi samfarin silifas.
Abubuwan sazaku tanada
Kwalin magwaji
Robar hancin takalmi
Roba tik
Roba sol
Igiya
Zamiya
Gam
Almakashi
Kwalin magwaji
Robar hancin takalmi
Roba tik
Roba sol
Igiya
Zamiya
Gam
Almakashi
Yadda zaku hada
Dafarko zaku samu kwalinku wanda zaku fidda surar takalmin dazaku hada, saiku sami wani takalmin wanda kukeso kasansa ya zama kamar wanda zakuyi, saiku dora akan kwalin nan sannan saiku bi ku zana da biro. Bayan kun zana saikusa almakashi ku yanke daidai kan biron.
Saiku dauki wannan kwalin da kuka yanko ku dora akan roba Tik ku kara tisawa da biro sannan saiku sa almakashi ku yanke. In kun tashi zaku fidda kafar dama da kafar hagu. Saiku kuma daukan wannan kwalin ku dora akan roba sol shima ku zana kafar dama da ta hagu.
To yanzu sai ku dauki wannan roba sol din ku auna incin 2 ba waya(kafa) 2 sai kuyi alama da biru a daidai tsakiyar takalmin inda zai tashi sakanin yan yatsun kafa da kuma babbar yatsa ta kafa. Bayan nan sai ku dawo kasan takalmin wajen dunduniya shima ku auna inchi 3 sai kuyi alama, sannan sai ku dan kara gaba kadan ku karayin wata alamar ku kara matsawa gaba kadan kuyi wata alamar (alama 3 za ai saboda igiyoyin takalmin huda 3 zamusa a kowacce kafa)
Sai ku dakko igiyoyin takalmin ku auna inchi 8 guda biyu, inchi 14 guda 6, wannan igiyoyi dasu zamuyi anfani wajen yin igiyoyin takalmin.
( Anan ya kamata ku dakata ku kalli videon dankuga yadda na kitsa wannan igiyoyi suka bani wannan suffar da kuke gani, ga link nan ku danna zai sadaku da videon https://youtu.be/lsZ47HMuGe0)
Bayan kun kitsa wannan igiya sai ku kama Bakin ku sanya cikin wannan hudoji da mukai na takalmin.
Sai ku samu san fefa ku goge jikin igiyoyin nan daidai inda zaku shafa gama sannan saiku fara kangawa ajikin kafarku dan ku san ko zaiyi maku cifcif ko akwai bukatar a rage ko a kara tsayin igiyoyin. (saboda wata kafar tafi wata tudu)
To bayan anyi wannan sai a shafa gam a kasan roba sol da kuma roba tik din (inda baida zane) da kuma jikin zamiyar tagaba da baya, sai a jingine abarshi ya sha iska. Yadda za a gane ya sha iska shine in aka taba da hannu za aji baya danko sai a dakkosu asawannan zamiyar a tsakiyansu wato roba sol da tik din saina manne. To bayan anyi wannan sai asa guduma adan bubbuga sama sama yadda zasu manne sosai.
To yanxu mun gama takalminmu sai kawai mu dauka mu kaiwa masu goge takalmi su gogo mana gabadaya zagayen takalmin yadda zai tashi kai daya. Wannan gugar batada tsada danmu nan suna goge mana akan naira 30. Kuma yawaici masu hada takalma ko gyaran takalma ne sukeyi. Duk wannan bayanin danai kuna iya kallonsa cikin video dan kufi fahimtar komai in sha Allah ,saiba danna wannan link din https://youtu.be/lsZ47HMuGe0 dan ganin videon.

No comments:
Post a Comment