Assalamualaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa iri daban daban da kanku cikin gidajenku kuma acikin sauki. Ayau in sha Allah zan koya maku yadda zaku dinka hular turban ne, kuma zaku nimi wayannan abubuwa kamar haka.
Abubuwan da zaku tanada
Yadi MAI karen miski (Velvet)
Tape
Almakashi
Zare da allura /keke
Fulawar ado (ba dole bane)
Yadda zaku dinka
Dafari zaku dauki tape sai ku auna yadin kamar haka (inchi 9 fadi, tsayi inci 11 ana yara) (inchi 11 fadi, tsayi inchi 13 Na manya) to sai Ku sa almakashi ku yanka sannan ku ajiye Agefe.
Sai Ku kumasa tape ku auna inchi 3 fadi tsayi kuma inci 6 kusa almakashi ku yanka (wannan guda biyu zakuyi) in ba a gane bayaninaba ku danna link din nan dan ganin yadda na yanyanka komai daki daki https://youtu.be/5nxEuplsx08
Bayan kun yanyanka saikuma ku dauki wannan siraran da muka yanka ba karshe guda 2 Ku ninkasu a tsaye yadda zaibada inchi 1½ a maimakon inchi 3 sai kusa almakashi ta daidai bakin ku yanka a karkace sannan ku dinkesu yadda zaibaku kusurwa (yanada kyau a kalli video din nan dan ganin yadda nai. Ku dannan link dan ganin videon https://youtu.be/5nxEuplsx08)
To yanzu sai ku dakko wannan yadi da muka fara yankawa (11 by 13) ku ninka shi a kwance yadda zai baku 11 by 6½ inchs. Sai ku dauki wannan siririn yadi da muka hada kusurwan dashi shima Ku ninka gida biyu sannan sai ku daidaitasu ku dinkesu atare yadda wannan kusurwa zata tashi a daidai tsakiyar wannan hula.
Bayan an dinke sai a dawa ta bayan hular (wato wajen keyan) sai asa zare da allura a tattare gefe biyun anma a rage kamar misalin inci 4. https://youtu.be/5nxEuplsx08 Ku danna link din kuga abinda nake nufi in ba a fahimtaba.
Yanzu sai a sa almakashi a yanko wani yadin mai fadi misalin inchi 20 tsayin kuma inchi 35 ko fi, yadanganta da iya sau nawa akeso a zagayo da daurin aka in anzo daurawa. To sai a zuro dashi ta daidai inda muka rage inchi 4 dinnan sannan asa keke a dinke.
Duk Wannan dinki in mutum baida keken dinki zai iya anfani da zare da allura wajen yinshi, sannan kuma yana da kyau a kalli videon da na hada da wannan rubutu dan afi fahimtar bayanin da nake. https://youtu.be/5nxEuplsx08 ga link din videon sai a danna a kalli videon.
No comments:
Post a Comment