Assalamualaikum yan uwa barkanmu da war haka, sannunmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa da Sana'oin hannu a gidajenku kuma cikin sauki.
Ayau zan koya maku yadda zaku hada abin adon bango wato wall hangings/ decor. wannan abun kwalliyar daki yanada matukar kawatawa kuma ana hada shi cikin sauki ba tareda an kashe kudi dayawa ba. Batare da bata lokaciba zaku bukaci abubuwan aiki kamar su.....
Abubuwan da zaku tanada
Cokula Na roba
Madubi (round)
Kwali
Penti (spray paint)
Faranti (circle)
Kyalli (glitters)
Almakashi
Gam (glue gun /stick)
Ribbon (ko bayis)
Yadda zaku hada
Dafarko idan zakuyi wannan abun adon bango zaku nimi cokula na roba sai kusa almakashi ku ciccire kan cokalin https://youtu.be/M1SAEbhAEec. Shi kuma ainihin marikin cokalin sai ku adana (badashi zamuyi anfaniba yau)
Sai Ku dakko kwalinku saiku ajiye akasa sannan saiku dakko faranti ku daura akai kubi jikin farantin da biru (tracing) in kin zana kusa almakashi ku yanka.
Sai Ku dauki wannan kwali da kuka yanka mai zagaye ku ajiye akasa sannan ku dakko madubinku ku daura akai, a daidai tsakiyar (ku tabbata mudubin baikai girman kwalinba) kina iya danna link dinnan dan ganin abinda nake nufi https://youtu.be/M1SAEbhAEec.
Bayan kun sa mudubin kun zana (tracing) a wannan karan bazaku sa almakashi ku yanka ba, sai Ku rika dakko wannan kan cokula da kuka yanyanke ku rika sa gam ta bayan cokalin sannan sai ku rika mannawa ajikin wannan kwalin(zaku fara daga daidai kan layin da kukaja na tsakiyar kwalin) wato dai dai inda zakusa madubin.
Haka zakuyi ta sa gam ajikin cokalin kuna mannawa har sai kun cike duka jikin kwalin sannan sai ku dakko penti ku shafe jikin wannan cokula dashi(har bayan kwalin)
Kafin ku fara fesa pentin yanada kyau ku shin fida kwali akasa saboda karya bata maku waje) bayan kun fesa pentin saikuma ku dakko kyalli ku yaryada akan wannan fenti da sauri kafin ya fara bushewa. Kuna sawa saiku sa gam a daidai tsakiyar kwalin sannan saiku daura mudubin, ku sa hannu kudan danna yadda zai kame.
Bayan kunyi wannan saiku juyo bayan kwalin ku dakko wannan ribbon ko bayis din ku sa gam ku manna da jikin kwalin yadda zai kame ajikin kwalin, to wannan dashi zaku manna abun adon bangon ajikin bango.
Wannan shine yadda zaku hada naku decoration din cikin sauki. Domin karin bayani kuna iya danna wannan link din https://youtu.be/M1SAEbhAEec dan ganin yadda na fara hada wannan abun decoration tundaga farko har karshe. Hakan zai kara baku daman fahimtar komai cikin sauki in sha ALLAH, shi yasa na dauki hoton komai cikin video yadda Za'aga komai. To sai mun hadu a wani darasin.
No comments:
Post a Comment