Assalamualaikum yan'uwa, ayau zamu koya maku yadda ake yin MANKWAKWA a gida.
Idan za Ai man kwakwa ana iya bin hanyoyin da dama wajen fidda man daga jikin kwakwa, anma ayau Zamuyi muku bayani akan yadda ake yinsa ta hanyoyin biyu in sha Allah.
hanaya ta farko (1)
Abun da zaku tanada:
Farin kwakwa
Wuka
Ruwa
Abin markade (blender)
Yadi ko rariya
Tukunya
Mazubi
Yadda ake yi:
Da farko zaku sami farin kwakwa, saina bare bawon sannan sai a yanyanka kanana yadda zai mana dadin markadawa.
Bayan mun yanka sai mu wanke sannan sai asa a abin markade a zuba ruwa wadatacce a markada sai yayi laushi.
Bayan an markada sai adau rariya mai laushi ko yadi irin na Tatar koko sai a tace wannan ruwan kwakwa da muka markada.dusar kuma in Anaso za a iyayin kwakumeti ko biskit Dashi.
Shi kuma wannan ruwan kwakwa sai a juye a tukunya a Dora akan wuta a barshi yayita tafasa (Anma kar a rufe tukunyar). Haka za a barshi harsai ruwan ya Kare gaba daya za a GA mai ya Fara fita, Sai a rage wutar a hankali za aga gaba daya ruwan ya kone.
Sai a kashe wutar abari ya huce sannan sai a dau rariya ko wani yadi mai kyau sai a tace. Sai a dau man da aka tace asa ajuye a mazubi, dattin da aka tace kuma sai a zubar.
No comments:
Post a Comment