Dinkin labule abune mai sauki wanda cikin dan kankanin lokaci za a iya yinsa. Labule na daga cikin kayan da suke kawata gidajenmu musanmam in akai anfani da yadi ko launi wanda yai daidai ya kuma haska wannan dakin da akai dominsa. A wannan karan zanyi maku bayanine akan hanyar da zakubi mafi sauki wajen dinkin kabulayenku da kanku a cikin gidajenku.
Abubuwan da zaku tanada.
Yadin labule
Tape mai zare
Tape na karfe ko lura
Karfen labule
Pin da keken dinki.
Yadda zaku dinka.
Da farko akwai bukatar ku auna kofa ko kuma tagar da zaku dinkawa labulen, ta hanyar anfani da tape. Wato zaku auna fadin kofar k nan da kuma tsayinta, dan ganin cikakken bayani akan yadda na auna kuna iya danna wannan link din https://youtu.be/HZnipJDVoW4 . Bayan kun auna Sannan saiku dakko yadin naku, misali in kun auna kofarku a kan inchi 5, to yanada kyau ku ninka awon yadda zai baku tattara bayan kun dinka, sai dai in mutum yafison labulen ya tashi ba tattara, ko da yake in akai mai tattarar yafi kyau.
Atakaiche dai shi dai fadin kofa ana sa yadi daya ne da rabi zuwa yadi biyu. Tsayin kuma ya danganta da iya tsayin kofarku. Sannan in aka tashi za ai dinkin gidan karfe na labule ana sa inchi 2 ne. A wannan videon nai bayani tare da nuna yadda nai dinkin labulen domin karin bayani. Ku dannan wannan link din, https://youtu.be/HZnipJDVoW4 dan ganin yadda nayi.
No comments:
Post a Comment