Wednesday, 28 February 2018

YADDA ZAKU MAGANCE KURAJEN FUSKA (PIMPLES)



Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da warhaka, ayau in sha Allah zamu duba daya daga cikin abubuwan da suke damun mafi akasarin mata musanman yanmata da mata masu karancin shekaru, Wannan abu kuwa shine kurajen fuska wanda ake kira da pimples.
 
Abubuwan da za'a tanada
Ruwan dumi
Sabulu
Lemon tsami (lemon)
Baking soda
Man zaitun.
Yadda zakuyi
Dafarko zaku samu ruwan dumi saiku wanke fuskarku da sabulu da wannan ruwa mai dumi.
Sai ku samu tawul ko wani yanki mai kyau ku goge fuskarku da shi.
Sai ku dauki lemon tsami (lemon) in babu sai kuyi da (lime) ku yanka gida biyu ku dauki rabin ku matse ruwan ku hada da baking soda (wannan dabanbanci da baking powder) misalin rabin karamin cokali saiku kwaba da kauri, sai ku shafa adaidai inda kurajen suke.
Sai ku barshi jikin fuskar sai ya bushe, bayan misalin minti 10 saiku dauki ruwa ku wanke fuskar dashi. Sannan sai ku goge da tawul ku shafa man zaitun.
Haka zakuyi kullum ko akalla sau 4 a sati. In sha Allah zakuga kurajen suna motsewa.
Wannan hanya in sha Allah in aka gwada za a dace, anma dole sai an kiyaye wasu halayya da mukeyi wanda mafi akasari yin hakan shine yake sawa kurajen su rika futowa. A gobe in sha Allah zamuyi bayani akan wannan halayya da muke da kuma hanyar magancesu.

Tuesday, 27 February 2018

YADDA ZAKU HADA JAKAR PAS (marar dinki)



 Ayau ma kamar yadda muka saba munxo maku da yadda zaku hada jakar hannu ta mata mai sauki wanda zakuyi ba tareda kunyi dinki ba, wannan jakar batada wuya kuma bata bukatar keke wajen hadata.
Abubuwan da zaku tanada
Cushion/mako/malha
Kwalin magwaji
Leda/fata
Yadin shafin jaka/satin
Maballi
Wuka
Gam
Almakashi
Zip (ba dole bane)
Yadda zaku hada
Dafarko zaku dauki kwalin magwaji sai ku yanka irin shape din da kukeso pas din ta bayar. Misali zaku dauki kwalin saiku lankwasa ta gida 3, kamar dai pas, to furkar saikusa almakashi ku yanka a karkace ko a gewaye.
  Bayan kunyi wannan saiku dakko malha ko cushion inchi 1 ko inchi 2 saiku dora wannan kwalin akai ku shata ku sa almakashi ku yanka sai ku ajiye a gefe.
  To sai ku dakko kwalin nan ku daura akan fatar/ledar da zakuyi jakar kusa biro ku shata, sannan saikusa almakashi ku yanke, anma in zaku yanke bazaku bi ta kan biron ba zaku dan matsa kadan misalin ½ichi.
  To shima yadin shafin haka zaku yankashi dai dai da wannan fata ko leda da kuka yanka. Sai ku dakko malhar nan ko cushion ku shafa mata gam shima fatar/ledar da zakuyi jakar ku shafa gam. Saiku ajiye ku bari ta bushe. In kun taba kunji baya kama hannu saiku mannesu waje daya (zakuga fatar yadanfi girma saiku lankwasata ku manne jikin malhan. Ku danna link dinnan kuga abinda nake nui anan acikin videon nan https://youtu.be/Y9ulCYVAzGE)
  To sai ku dakko kwalin magwajin nan da yadin shafin suma ku shafa masu gam, a gefe guda guda, insunsha iska saiku mannesu, shima yadin sai alankwasa ajikin kwalin.
  To yanzu sai mu dakko wannan fatar da malhar da muka manne mu shafa gam ajikin malhar, shima mai yadin shinan da kwali sai a shafa gam ajikin kwalin sai abarshi yasha iska, sannan sai a mannesu (anan yanzu zamu mana maballanmu kafin mu manne gaba daya) zamuyi anfani da wuka mu dan huda sai mu manna) ku danna link din kuga yadda na manna https://youtu.be/Y9ulCYVAzGE
  Yanzu saura cikin jakar. Wannan pas din mai wallet ne shi yasa bama bukatar ai masa makari a gefe, anma nan gaba zan nuna maku yadda zakuyi mai makarinma in Allah ya yarda.
  Sai ku yanko yadi daibdai da fadin tsakiyar pas din (kunsan mun lankwasata gida uku da fari) sai ku yanka yadin gida biyu ta sama kusa zip, anma wannan ba dole bane, in kunaso kuna iya lankwasawa kawai kuyita hawa hawa kamar yadda akeyin maajin id card acikin wallet. Saiku shafa gam a zagayen jakar, iya inda zaku manna aljihun, inya bushe sai ku manna. In kunaso zaku iya dan kara wani yadin yayin mannewa saiku rika sa chain/sarka irin hannun jakar nan na suwaga. Wannan bayanin da nake gaba daya na nunashi dalla dalla acikin videon nan, kudai ku dannan link kawai ku sha kallo https://youtu.be/Y9ulCYVAzGE

Monday, 26 February 2018

YADDA ZAKU DINKA JAKA MAI SAUKI (ba zip ba shafi )





Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa acikin wannan fili namu da muke koya maku yadda zaku harhada abunuwan anfaninku da iyalanku a cikin gidajenku kuma cikin sauki. Ayau zan nuna maku yadda zaku dinka jakane mai sauki, saboda wannan jakar ba a bukatar ai mata wani dinke dinke mai yawa a jikinta.
Abubuwan da zaku tanada
Leda/fata
Tape
Almakashi
Yadda zaku hada.
Dafarko zaku dauki tape sai ku auna inchi 14 zuwa 16 fadi, tsayi kuma inchi 26 zuwa 28 (zaku iya karawako ku rage, wannan ya danganta da iya yadda kukeson girman jakar ta kasance.
  Saiku ninkata a kwance (yadda zurfin jakar zai bada inchi 13 zuwa 14) sannan saiku dauki tape ku fara aunawa daga kasan jakar ( inchi 3)  ta gefe guda, sai kuyi alama, sannan sai ku kuma auna inchi 3 a kwance daga dai kana jakar, sannan sai ku sa almakashi ku yanke yadda zai tashi kamar kwana. To yadda kukayi wannan haka zaku kuma maimaitawa a dayan gefenma. (nan wajen yanada dan wuyan fahimta ta hanyar bayani da baki shi yasa yanada kyau ku kalli videon nan dan ganin yada zakuyi cikin sauki https://youtu.be/X5tii-94p-M ku dannan link din ku gani.
  To bayan kun yanke kwanar guda biyu, saiku jiyu da jakar ta baibai ku dinko gefen jakar guda biyu, daga saman jakar har iya inda mukai wannan kwanar. Sannan sai ku kama wanan kwanar da mukai shima ku juyata a kwance yadda dinkin nan na gefen jakar zai tashi a tsakiya, sannan saiku dinkata........  Nan wajenma zaku fi fahimta in kuka kalli videon.
   To bayan anyi wannan shike nan sai ku juyo da jakar dai dai, in kunaso zaku iyayi mata kalmasa ta bakinta, anma ni banyiba. To sai a yanko hannayen jakar yanzu.
   In an tashi za ai hannu zaku iyayin mai tsayi ko guntu, ya danganta da yada kukeso, anma akalla zakusa daga misalin inchi 26 zuwa 36, fadin kuma sai ku sa inchi 1½  in bazakuyi kalmasa ba, anma in zakuyi shima zakusa akalla inchi 3.
  To bayan kun yanko wannan guda biyu. Saiku dinketa jikin jakar. Anma kafin ku dinke yanada kyau ku auna daga saman jakar zuwa daidai inda zaku manna dan kar wani yafi wani, hakama fadin gefen jakar. Duk wannan bayanin danai zaifi kyau ku hada da videon dan shine zai baku daman gani da kuma gane yadda zakuyi ku dinka kamar yadda na nuna. Ku danna link dinnan dan ganin videon https://youtu.be/X5tii-94p-M

Wednesday, 21 February 2018

YADDA ZAKU HADA TAKALMI MAI TUDU

Assalamu alaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa acigaba da kawo maku dabarun harhada abubuwa cikin sauki da kanku kuma acikin gidajenku. Ayau zan nuna maku yadda zaku hada takalmi mai tudu wanda akekira da kito ko wedges.
 
  Abubuwan da zaku tanada
Kwalin magwaji
Roba tik
Roba cushion
Almakashi
Yadi
Gam
Kibiya
Wuka
Yadda zaku hada
Dafarko in zaku hada wannan takalmi zaku samu wani takalmi wanda siffarsa tai yanayi da irin wannan da zamuyin. Sai ku daurashi a kan kwalin magwaji ku zana sannan kusa almakashi ku yanke.
   Bayan kunyi wannan saiku dauki wanan kwali ku daura akan roba tik kubida biro ku fidda suffar wannan takalmi (gaba daya kafar hagu da daman)
  Sai ku dakko roba cushion shima ku dora wannan kwali akansa ku zana sannan saiku yanke da almakashi. Anan zaku iya anfani da roba cushion kala 2 kamar yadda nayi, in kunaso zaku iyasa kala 3 koma 4. Sannan zaku iya sa hawa 2,3 ko 4 kamar yadda nayi. Abin lura kawai shine iya tudun da kukeso wannan takalmi ya baku iya hawa nawa zaku dora wannan roba cushion.
  Bayan kun fidda roba cushion dinda roba tik saiku dauki roba cushion wanda zai zama shine a saman takalminku ku auna inchi 2.7 daga sama wajen yatsu saiku sa kibiya ku huda, to anan zamusa igiyar takalmin. Saikuma mu koma can kasa wajan dunduniya mu auna inchi 3 sai mu yi alama ta gefe da gefen takalmin wato inda zamusa ragowar igiyoyin takalmin. Sai musa wuka mu tsaga dai dai fadin igiyar takalmin da zamuyi anfani dashi.
  To yanxu sai mu samu wani yadin wanda zamuyi igiyar takalmin dashi sai mu yanko kamar misalin inchi 6 da kuma wani misalin inchi 10 sai mu hadasu mu daure (ku duba link dinnan dan ganin yadda na daure nawa cikin video https://youtu.be/dEmWSO-qEY4)   To bayan kun daure saiku zura wannan igiyoyi cikin roba cushion din da kuka huda kamarbdai yadda na nuna acikin videon.
To yanzu sai mu dakko wannan roba tik mu shafa masa gam (gefen da ba zane) suma roba cushion din mu shafa gam, mu bari yasha iska kafin sai mu dakkosu mu jejjera yadda zai bamu hawa hawan da mukeso. Bayan mun jera sai mukai wajen masu gugan takakmi su gogo mana gefe gefen yadda zai tashi gaba daya kai daya. Shike nan mun gama takalminmu. Yanada kyau a kalli videon nan dan ganin yadda na fara hada takalmin da yadda ma ake goge takalmin , https://youtu.be/dEmWSO-qEY4 ku danna wannan link din kuga videon.

Tuesday, 20 February 2018

YADDA ZAKU HADA TAKALMI SILIFA



Assalamualaikum yan'uwa barka da warhakav ayau in sha Allah zamuyi bayanine akan yadda ake hada takalmi samfarin silifas.
Abubuwan sazaku tanada
Kwalin magwaji
Robar hancin takalmi
Roba tik
Roba sol
Igiya
Zamiya
Gam
Almakashi
Yadda zaku hada
Dafarko zaku samu kwalinku wanda zaku fidda surar takalmin dazaku hada, saiku sami wani takalmin wanda kukeso kasansa ya zama kamar wanda zakuyi, saiku dora akan kwalin nan sannan saiku bi ku zana da biro. Bayan kun zana saikusa almakashi ku yanke daidai kan biron.
Saiku dauki wannan kwalin da kuka yanko ku dora akan roba Tik ku kara tisawa da biro sannan saiku sa almakashi ku yanke. In kun tashi zaku fidda kafar dama da kafar hagu. Saiku kuma daukan wannan kwalin ku dora akan roba sol shima ku zana kafar dama da ta hagu.
  To yanzu sai ku dauki wannan roba sol din ku auna incin 2 ba waya(kafa) 2 sai kuyi alama da biru a daidai tsakiyar takalmin inda zai tashi sakanin yan yatsun kafa da kuma babbar yatsa ta kafa. Bayan nan sai ku dawo kasan takalmin wajen dunduniya shima ku auna inchi 3 sai kuyi alama, sannan sai ku dan kara gaba kadan ku karayin wata alamar ku kara matsawa gaba kadan kuyi wata alamar (alama 3 za ai saboda igiyoyin takalmin huda 3 zamusa a kowacce kafa)
Sai ku dakko igiyoyin takalmin ku auna inchi 8 guda biyu, inchi 14 guda 6, wannan igiyoyi dasu zamuyi anfani wajen yin igiyoyin takalmin.
( Anan ya kamata ku dakata ku kalli videon dankuga yadda na kitsa wannan igiyoyi suka bani wannan suffar da kuke gani, ga link nan ku danna zai sadaku da videon https://youtu.be/lsZ47HMuGe0)
Bayan kun kitsa wannan igiya sai ku kama Bakin ku sanya cikin wannan hudoji da mukai na takalmin.
  Sai ku samu san fefa ku goge jikin igiyoyin nan daidai inda zaku shafa gama sannan saiku fara kangawa ajikin kafarku dan ku san ko zaiyi maku cifcif ko akwai bukatar a rage ko a kara tsayin igiyoyin. (saboda wata kafar tafi wata tudu)
  To bayan anyi wannan sai a shafa gam a kasan roba sol da kuma roba tik din (inda baida zane) da kuma jikin zamiyar tagaba da baya, sai a jingine abarshi ya sha iska. Yadda za a gane ya sha iska shine in aka taba da hannu za aji baya danko sai a dakkosu asawannan zamiyar a tsakiyansu wato roba sol da tik din saina manne. To bayan anyi wannan sai asa guduma adan bubbuga sama sama yadda zasu manne sosai.
  To yanxu mun gama takalminmu sai kawai mu dauka mu kaiwa masu goge takalmi su gogo mana gabadaya zagayen takalmin yadda zai tashi kai daya. Wannan gugar batada tsada danmu nan suna goge mana akan naira 30. Kuma yawaici masu hada takalma ko gyaran takalma ne sukeyi. Duk wannan bayanin danai kuna iya kallonsa cikin video dan kufi fahimtar komai in sha Allah ,saiba danna wannan link din  https://youtu.be/lsZ47HMuGe0 dan ganin videon.

Monday, 19 February 2018

YADDA ZAKUYI TAKALMI MAI BEADS



Assalamu alaikum yan uwa, barkanmu da warhaka. Kamar kullum yauma mun taho maku da yadda zaku hada takalman nan masu beads cikin sauki kuma acikin gidajenku.
Abubuwan da zaku tanada
Beads
Allura
Zaren/ robar beads
Takalmi silifas
Sai gam
Yadda zaku hada
Dafarko zaku wari zare ko robar yin shiri wato nayin beads wadatacce sai ku sanya cikin allura. Sai ku dauki takalmin ku zura allurar ta saman takalmin daidai inda yake zama a tsakakkanin babban yatsar kafa da sauran yastun kafar. Saiku bullo dashi ta kasa sannan ku kuma tsirawa ku maido da allurar tabbullo sama kamar dai za ai dinki. (akwai video yanada kyau ku duba saboda ku kara fahimtar bayani na )
  Bayan kun ziro zaren sai ku ajiye takalmin a gefe, sannan ku sake yankan wani zaren ku kirga beads guda 6 sai kubzira acikin wannan zaren da kuka yanko, sai ku kama bakin zaren dayake hannunku na dama ku shigar dashi cikin beads din da yake hannunku na hagu.
Shikuma zaren da yake hannunku na hagu sai ku shigar dashi cikin beads din da yake hannunku na dama. In kukai haka zai baku round kamar fulawa. (https://youtu.be/3pybox7OyJs adanna link dan ganin abinda nake nufi)
  To haka zakuyi tayi har sai kunyi kamar guda 8 ko 6 sai ku dauki ko wani guda daya da kukayi ku rika dinkawa a jikin igiyar takalmin nan da zare da allura (anmafa zaren roba nayin shiri) idan kunaso zaku iyayi ajikin igiya daya kamar yadda nayi ko kuyi ajikin dukka igiyoyin guda biyu. Yanada kyau ku kalli videon shine zaisa ku fi fahimtar yadda zaku dinka beads din a jikin takalmin cikin sauki.
   To bayan kun dinka wannan sai ku dauki wani beads din (sosamu kusa wayanda suka fi na farkon girma) saiku rika diga gam wanda akesawa da bindiga sannan ku dora beads din akai. Kamar yadda nanuna acikin videon.
   To in a jikin igiya daya kukayi dinkin beads din nan masu fulawa, saiku dauki dayan beads din manya ku dinkasu suma ajikin sauran igiyoyin takalman. Adanna link din nan dan ganin bayanin yadda na fara sanya beads din har karshe https://youtu.be/3pybox7OyJs

Wednesday, 14 February 2018

YADDA ZAKU HADA MADAURIN KAI NA MATA (HEAD BAND)



Assalamualaikum barkanmu da warhaka, ayau in sha ALLAH zamuyi bayani akan yadda zaku dinka abin adon mata na kai wato head band, wannan zamu koyar da iri biyu ne anma kusan dayane saboda banbancinsu bamai yawa bane.

Abinda zaku tanada
Yadi mai roba
Zare da allura
Beads
Botir
 
Yadda zaku dinka (1)
Dafarko za'a auna ko inci nawa akeson tsayin wannan band din, wannan zan muku misali dana yara yan shekara 8-12,  in kuna so kuyi na manya saiku kara awon, in kuma na jarirai ne sai ku rage. Abi mafi sauki wajen sanin iya adadin daza asa shine a dauki tape a zagaya kan yarinyar da za aiwa sai asan nawa ne inchin da za asa.
To kamar yadda nai bayani wannan zamusa inci 20 tsyin fadin kuma inchi 9, sai a ninka a tsaye yadda zaibada 20by4½. Sai a dinke gefen yadda zai tashi dogo kamar safa anma bakin 2 abude.  Sai asa hannu a juyo dashi dai dai.
  Bayan anyi wannan saikuma akama bakin guda biyu asa zare da allura adinkesu (adanna link din nan dan ganin yadda za a dinke https://youtu.be/xax478NYRWI)
  To sai kuma a dakko Beads din shima ayi anfani da zare da allura a dinke adaidai saitin inda muka dinke din nan yadda zai zamana beads din sun rufe dinkin ba a ganin sa gaba daya (Ku danna link dan a kalli videon dan fahimtar abunda nake nufi anan https://youtu.be/xax478NYRWI)
Yadda za ku hada (2)
Wannan shima kamar wancen zaku auna ku yanka ku kuma dinke gefensa sannan ajuyo dashi dai dai.
To sai akama bakinsa guda 2 adinke da keke ko da zare da allura. Sai a yanko wani yadin kamar misalin inci 3 fadi da tsayinsa sai aninka shi 2 a dinke gefe daya sai shima asa hannu ajuyo dashi daidai sannan sai a daukeshi arufe wannan dinki da mukai na tsakiyan dashi. Shima a dinke nasa bakin https://youtu.be/xax478NYRWI Ku danna link din dankuga abinda nake nufi anan.
  To sai a dakko botir din, sai asa da gam ko da zare da allura agaban band din. Shikenan.
  Adanna link din akalli videon dan ganin irin yadin da botir din da nayi anfani da.
https://youtu.be/xax478NYRWI

Tuesday, 13 February 2018

YADDA ZAKU DINKA HULAR TURBÄN (2)

Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da warhaka. Ayau zamuyi bayani akan yadda zaku dinka turban a karo Na biyu, wannan hular yanayin dinkinta akwai banbanci dawacen da mukai na farko.

Abubuwan da za a tanada
Yadi mai karen miski
Tape
Almakashi
Zare da allura
Keken dinki.

Yadda za ayi
Dafarko za'a fara da auna tsayi da fadin yadin daza ai anfani dashi. A wannan zamuyi amfani Da inchi 40 A tsayin, fadin kuma inchi 12.
To bayan mun auna munsa almakashi muna yanki iya abuda zamu bukata to sai a ninka shi gida biyu a kwance (wato ya zama 20 by 12) sai a dinke gefe 3, dayan gefen shima za a dinke anma za abar fili misalin inci 2½ a farko da karshen wannan gefen (to nan baza a dinke ba)  yana da kyau akalli vidion dan ganin inda za a dinke din da kuma inda za a tsallake, ga link din https://youtu.be/IktQIe4qlAo a danna sai a kalli videon.
  To bayan an dinko sai a kama tsakiyar wannan yadi da muka dinko a tura gefe daya cikin daya gefen, yadda zai tashi kamar buhu, kuma wannan fili da muka bari bamu dinkeba (inchi 2½) zasu koma guri guda. Adanna link dan ganin abinda nake nufi anan https://youtu.be/IktQIe4qlAo
  To yanzu sai a kuma yanko wani yadin misalin inchi 7 fadi tsayi kuma inchi 8 sai a ninka a tsaye a dinke gefen sannan sai asa hannu a juyo dashi dai dai. Sai a dauki wannan hula da muka fara sai asa hannu ta cikin wannan huda a zuro wannan yadi mai inchi 7by 8 a hade bakinsa a dinke ta cikin hular. (wannan waje yanada kyau a tsaya a kalli videon dan afi fahimtar bayanina, ga link ku danna ku gani https://youtu.be/IktQIe4qlAo)
To da anyi wannan sai a jiyo bayan hular asa zare da allura ta daidai saman hular a yi tattara daga sama zuwa kasa ta wajen keyar k nan (anma za abar misalin 2½) sai atsaya anan atisa dinkin yadda bazai ware ba.
Da anyi wannan shi kenan za aga hular ta fito dai dai da irin wannan na jikin hotan, domin ganin yadda na dinka nawa daga farko har zuwa karshe saiku danna wannan link din https://youtu.be/IktQIe4qlAo.

Monday, 12 February 2018

YADDA ZAKU DINKA HULAR TURBÄN (1)

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa iri daban daban da kanku cikin gidajenku kuma acikin sauki. Ayau in sha Allah zan koya maku yadda zaku dinka hular turban ne, kuma zaku nimi wayannan abubuwa kamar haka.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi MAI karen miski (Velvet)
Tape
Almakashi
Zare da allura /keke
Fulawar ado (ba dole bane)

Yadda zaku dinka
Dafari zaku dauki tape sai ku auna yadin kamar haka (inchi 9 fadi, tsayi inci 11 ana yara)  (inchi 11 fadi, tsayi inchi 13 Na manya) to sai Ku sa almakashi ku yanka sannan ku ajiye Agefe.
Sai Ku kumasa tape ku auna inchi 3 fadi tsayi kuma inci 6 kusa almakashi ku yanka (wannan guda biyu zakuyi) in ba a gane bayaninaba ku danna link din nan dan ganin yadda na yanyanka komai daki daki https://youtu.be/5nxEuplsx08
Bayan kun yanyanka saikuma ku dauki wannan siraran da muka yanka ba karshe guda 2 Ku ninkasu a tsaye yadda zaibada inchi 1½ a maimakon inchi 3 sai kusa almakashi ta daidai bakin ku yanka a karkace sannan ku dinkesu yadda zaibaku kusurwa (yanada kyau a kalli video din nan dan ganin yadda nai. Ku dannan link dan ganin videon https://youtu.be/5nxEuplsx08)
  To yanzu sai ku dakko wannan yadi da muka fara yankawa (11 by 13) ku ninka shi a kwance yadda zai baku 11 by 6½ inchs. Sai ku dauki wannan siririn yadi da muka hada kusurwan dashi shima Ku ninka gida biyu sannan sai ku daidaitasu ku dinkesu atare yadda wannan kusurwa zata tashi a daidai tsakiyar wannan hula.
  Bayan an dinke sai a dawa ta bayan hular (wato wajen keyan) sai asa zare da allura a tattare gefe biyun anma a rage kamar misalin inci 4. https://youtu.be/5nxEuplsx08 Ku danna link din kuga abinda nake nufi in ba a fahimtaba.
  Yanzu sai a sa almakashi a yanko wani yadin mai fadi misalin inchi 20 tsayin kuma inchi 35 ko fi,  yadanganta da iya sau nawa akeso a zagayo da daurin aka in anzo daurawa. To sai a zuro dashi ta daidai inda muka rage inchi 4 dinnan sannan asa keke a dinke.
  Duk Wannan dinki in mutum baida keken dinki zai iya anfani da zare da allura wajen yinshi, sannan kuma yana da kyau a kalli videon da na hada da wannan rubutu dan afi fahimtar bayanin da nake.  https://youtu.be/5nxEuplsx08 ga link din videon sai a danna a kalli videon.
 

Wednesday, 7 February 2018

YADDA ZAKU DINKA TURO FILON SARAKAI

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da warhaka, ayau zamu koya maku yadda zaku dinka turofilo (throw Pillow) irin na sarauta.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi (mai karen miski)
Fiber dan duri
Botir 2
Tape
Zare da allura
Almakashi

Yadda zaku dinka
Dafarko zaku auna tsayi da fadin da kukeson filon ku ya kasance, wato in babba zakuyi ko karami, misali in kukasa tsayin yadin inchi 45 to fadin zakusa inchi 20 (in kunaso yayi tudu) anma in bakwasonsa da tudu saikusa inchi 17 amaimakon 20.
Bayan kun auna saikusa almakashi ku yanka sannan sai ku kama bakin yadin guda biyu ku ninka gida 2 (yadda zaibaku inchi 20 by 22½) idan ba'a fahimci bayaninaba a danna link dinnan https://youtu.be/3G2DJGIDiQo dan ganin abinda nake bayanin cikin hotan video)
  To bayan an ninka sai a hau keke a dinke gefe guda yadda zai tashi kamar siket, wato sama a bude kasama abude. Saikuma ku dauki zare da allura (ayi anfani da zare mai karfi kamar lilo/silo) sai ku kama saman yadin ku yi yar tattara (wato ku rika shiga kuna fita da zaren har ku zagayo inda kuka fara) in kun zagayo saiku zuge bakin ku dinke ruf yadda bazai rika budewa ba.
  To sai ku kuma Maimaita tattatar a daya bakin yadin, anma wannan karan bazaku zuge bakin kamar yadda mukai Afarko ba. Za a barshi yadda zamu iya dura fibet acikine.
  Bayan kunyi wannan zai tashi kamar buhu, saiku ibi fiber ku dura aciki iya yadda kukeso ku cikashi sannan sai ku kama zaren da allurar ku karasa tattare saman wannan bakin filo da mukeyi kamar dai yadda mukai na farko, shima a tsukeshi sosai a dinke yadda bazai budeba.
  Kuna yin wannan zakuga ya baku suffar wannan filo to anma bazamu bashi hakaba, sai kuma a dakko wayannan botirar asa ta saman pilon sannan a ziro da allurar ta tsakiyan filon ya bullo ta kasan sai a kuma sa dayan botir din akuma maimaitawa (yanada kyau adan matse hannu wajen wannan dinkin.
  Ku danna wannan link din dan ganin videon yadda na hada nawa filon https://youtu.be/3G2DJGIDiQo

YADDA ZAKU DINKA TURO FILON SARAKAI

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da warhaka, ayau zamu koya maku yadda zaku dinka turofilo (throw Pillow) irin na sarauta.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi (mai karen miski)
Fiber dan duri
Botir 2
Tape
Zare da allura
Almakashi

Yadda zaku dinka
Dafarko zaku auna tsayi da fadin da kukeson filon ku ya kasance, wato in babba zakuyi ko karami, misali in kukasa tsayin yadin inchi 45 to fadin zakusa inchi 20 (in kunaso yayi tudu) anma in bakwasonsa da tudu saikusa inchi 17 amaimakon 20.
Bayan kun auna saikusa almakashi ku yanka sannan sai ku kama bakin yadin guda biyu ku ninka gida 2 (yadda zaibaku inchi 20 by 22½) idan ba'a fahimci bayaninaba a danna link dinnan https://youtu.be/3G2DJGIDiQo dan ganin abinda nake bayanin cikin hotan video)
  To bayan an ninka sai a hau keke a dinke gefe guda yadda zai tashi kamar siket, wato sama a bude kasama abude. Saikuma ku dauki zare da allura (ayi anfani da zare mai karfi kamar lilo/silo) sai ku kama saman yadin ku yi yar tattara (wato ku rika shiga kuna fita da zaren har ku zagayo inda kuka fara) in kun zagayo saiku zuge bakin ku dinke ruf yadda bazai rika budewa ba.
  To sai ku kuma Maimaita tattatar a daya bakin yadin, anma wannan karan bazaku zuge bakin kamar yadda mukai Afarko ba. Za a barshi yadda zamu iya dura fibet acikine.
  Bayan kunyi wannan zai tashi kamar buhu, saiku ibi fiber ku dura aciki iya yadda kukeso ku cikashi sannan sai ku kama zaren da allurar ku karasa tattare saman wannan bakin filo da mukeyi kamar dai yadda mukai na farko, shima a tsukeshi sosai a dinke yadda bazai budeba.
  Kuna yin wannan zakuga ya baku suffar wannan filo to anma bazamu bashi hakaba, sai kuma a dakko wayannan botirar asa ta saman pilon sannan a ziro da allurar ta tsakiyan filon ya bullo ta kasan sai a kuma sa dayan botir din akuma maimaitawa (yanada kyau adan matse hannu wajen wannan dinkin.
  Ku danna wannan link din dan ganin videon yadda na hada nawa filon https://youtu.be/3G2DJGIDiQo

Tuesday, 6 February 2018

YADDA AKE DINKIN FILO MAI SUFFAR TATTASAI

Assalamualaikum yan uwa barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku yadda zaku rika harhada abubuwa da kanku cikin sauki. Ayau zan nuna maku yadda zaku dinka filo mai suffar tattasai.

Abubuwan da zaku tanada
Yadi mai karen miski (Velvet)
Fiber dan duri
Zare da allura
Almakashi

Yadda zaku hada
Dafarko idan zakuyi wannan filo zaku shimfida yadinku a kasa sai ku ninka biyu anma a karkace yadda zai baku shape din kwarkwaro ko bututu (ku danna link dan ganin yadda zaku ninka https://youtu.be/oQcXNgPXYx8)
Bayan kun ninka saikuma kusa almakashi ku yanke ta saman iya tsayin da kuke so kuyi.
Saiku dauki wannan mai kamar kwarkwaron saiku ninka shi ta baibai sannan sai ku dinkeshi  a tsaye yadda zai tashi kamar dai yadda kwarkwaro yake (nayin kunshin fulawa)
To sai ku dakko zare da allura ku kama saman wannan kwarkwaro inda yake da fadi ku rika sa allurar ciki kuna fita kamar zakuyi tattara. Sai kuyi ta tatarewa har ku zagaye saman wannan kwarkwaron. To sai ku dakko fiber ku dura a ciki sannan saiku xuge bakin kwarkwaron (kuna zugewa zakuga ya baku suffar tattasai)
  To sai ku dakko wani yadin karami shima kuyi mar kamar yadda mukai Na farkon (wannan shine hancin tattasan, shima bayan an dinke za ai duri a zuge.
Yobisi kuma ku dauki kallar yadin da kukayi hancin tattasan ku fidda suffar ganye a jiki, in kunaso zaku iya mar duri shima ko kuma ku barshi hakannan.
  To yanzu saiku dakko tattasan ku sa hancin tattasan da kuma ganyen ku hadesu jikinsa a zare da allura. Yana da kyau ku kalli videon dan ganin yadda nayi wannan filon, domin ganin yadda na hada ku danna link dinnan https://youtu.be/oQcXNgPXYx8
Sai mun hadu a wani filon in sha ALLAH.

Monday, 5 February 2018

YADDA ZAKUYI PILLOW MARA DINKI

Assalamualaikum yan uwa, barkanmu da warhaka, Ayau darasinmu zamuyi akan throw Pillow ne wanda in za ayi ba'a bukatar gam, zare da allura ko keken dinki wajen hadashi.

abubuwan da za a tanada
Yadi mai tsantsi (satin)
Pillow mai kwana 4

Yadda ake hadawa
Da farko za a tanadi pilow wanda yake mai kwana 4, in ba ada pillo sai a dinka daya, saboda wannan wanda zamuyi zai zama kamar gidan pilo ne zamuyiwa pilon.
To sai a dakko yadin a shimfida a kasa,  yadin ya zamana duk gefen hudun kansu daya, misali in inchi 20 ne saman to kasan ma haka za asa gefe da gefenma haka za asa.
Sai a dakko pilon asa a tsakiya anma akarkace (aduba wannan Link din dan ganin hotan yadda za asa pillon https://youtu.be/sjf2U6VphXc)
Bayan ansa sai a kama leben yadin guda biyu a lankwasosu a tura kasan wannan pilon,  ku duba videon dan ganin yada ake turawar dan bazai bayanu da baki ba) bayan anyi wannan sai kuma a dakko dayan bakin yadin guda 2 sai a kama a daure (kamar yadda ake daure abincin sallah acikin dankwali muna yara 😀)
In an daure sai kuma a gyara gun da aka daure. In anaso sai abarshi haka in kuma anaso sai asamu wani yadin (ni nasa ruwan hoda)  sai shima a daure akan wancan kullin da akai na farko.  Sannan sai a juya kullin yadda kullin zai koma ciki.
Wannan shine yadda ake yin wannan pilon, yanada kyau a kalli videon dan ganin yadda na hada komai cikin sauki, ku danna link dan gannin videon https://youtu.be/sjf2U6VphXc.
In an tashi za a wanke pillon saidai kawai a kwance daurin a wanke in ya bushe a goge a kuma daurewa.

YADDA AKE HADA MAN KITSO

https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs