koyi yadda zaka/ki harhada kayan anfanin gida da dabarun kirkirar kayan adon daki harma da sanaoin hannu tare da rahhaj cikin sauki. domin kasancewa damu ku duba youtube channel dinmu dan ganin videos dinmu.
Sunday, 13 December 2020
Sunday, 25 October 2020
Monday, 10 August 2020
Friday, 17 July 2020
GYARAN GIDA / SIRRIN GYARAN DAKI
kun taba samun kanku a yanayin da zai zamana kunyi GYARAN guru anma cikin Dan kankanin lokaci gurin ya kuma hargitsewa kamar ma bakuyiba ? sau tari zakuga mun gyara drowar mu ko ta yara anma cikin kwanaki kadan sai duk ya hargitse kamar ma bamuyi ba, to a wannan videon nawa zan nuna maku dabarar dazaku rika bi Dan samun damar kawar da wannan matsalar cikin sauki. karku manta Ku danna subscribe sannan Ku dannan kararrawar da take kusa da ita Dan samun sababbin bidiyos dina dazarar na daura.
Ku danna wannan link din Dan ganin bidiyon.
https://youtu.be/IX5CEZguEfA
GYARAN JIKI / MAIDA TSOHUWA YARINYA
Hanyoyin gyaran jiki Nada yawan gaske, anma wannan haya da zaku yi magana akai ayau nadaga cikin hanyoyin mafi amincewa da masana sukai magana akai na magance matsalal bushewa da yankwanewar fata Wanda ake kira da tamoji.
Matsalal tamoji basai ga tsofaffi ba kawai, hatta masu karancin shekaru sukan tsinci Kansu cikin wannan matsala na yankwanewar fata. Wannan yasa a yau zan nuna maku hanyar da zaku bi Dan magance wannan matsalar ta hanyar Amfani da ayaba da kuma wasu sinadarai.
Ayaba na dauke da sinadarai masu karawa fata lafiya, hakan yasa ake Amfani da shi wajen warware wannan matsalar. A wannan bidiyon na warware sirrin dake kunshe cikin ayaba dama yadda ake hada wannan sinadarin. Ku danna link din nan
👉 https://youtu.be/pkDtTSvrgdA
Dan ganin yadda ake yi. Kuna iya ziyartar shafina dake YouTube mai suna rahhaj DIY Dan ganin wasu bidiyon da dama Wanda nake koyar da gyaran jiki dama sana oin hannu.
GYARAN JIKI / MAGANIN RAGE KIBA
A wannan bidiyon nayau zamu duba amfanin amfani da sinadarai da yayn itatuwa wajen gyaran jiki. Ruwan yayan itatuwa Nada kyau sosai wajen gyara fata, masana sun tabbatar da amfani da wayannan sinadarai kadai na taimakawa wajen wanke maikon ciki tare da kauda matsalar teba ko tumbi.
Abubuwan da zamuyi Amfani da a yau sune kokumba, citta, lemon tsami da kuna na' a na 'a. Ku danna wannan link din Dan ganin yadda ake yi 👉 https://youtu.be/ZrnM7p596XE
https://youtu.be/ZrnM7p596XE
GYARAN JIKI DA DANKALI
YADDA AKE KARA HASKEN FATA
A wannan bidiyon zan nuna maku hanya mafi sauki da safta na kara hasken fata ba tare da kunyi bleaching ba. Wannan hanya da zan nuna maku a yau, ba wai kawai zai saku haske bane, A A, yana magance matsalolin fata kamar kuraje, tabo da sauransu.
Idan za ai wannan sinadarin gyaran fatan, za a nimi dankali. Anma ba ko wanne irin dankali ba. Wannan ana Amfani da dankalin turawane wato Irish. Ku danna wannan link din Dan ganin bidiyon yadda ake yi
👉 https://youtu.be/oVbF3V7Agv4
Kuna iya ziyartar shafina dake YouTube mai suna rahhaj DIY Dan ganin wasu bidiyoyin na gyaran jiki da koyan sanaoin hannu.
YADDA AKE GYARAN KAFA
Gyaran jiki yana da kyau, anma bai tsaya iya gyaran fuska ba, kafama Nada kyau ya zamana ana gyarawa akai akai. Rashin gyaran shi yake haifar da matsalolin fatan kafa kamar su Faso, kaushi da waskanai.
A wannan bidiyon nawa zan nuna maku yadda zaku yi Amfani da sinadarai namu na cikin gida Dan gyaran kafafunku. Wayannan sinadarai sun hada da gishiri, bakar soda, sabulun shampoo da sauransu.
Domin ganin yadda ake hada wannan sinadarai Ku danna nan
👉https://youtu.be/yWdoYUEFkII. Sannan kuna iya ziyartar shafinmu dake YouTube mai suna rahhaj Diy Dan ganin wasu hanyoyin gyaran jikin, dama yadda zaku koyi sana aoin hannu da dama.
MAGANIN ZUBEWAR GASHI
Dayawayawan mu mata bawai bamuda gashi bane, matsalar kawai gashinne bai zama, nan da nan ya karye ya lalace, wannan yana faruwa ta dalilin rashin gyara kokuma rashin San in hanyoyin da zamu bi Dan maganace wannan matsalar.
A wannan videon nawa na yau zan nunamaku hanyar da zakubi wajen kare gashin Ku daga zubewa, da kuma karyewa cikin sauki. wannan sirrin yana kara wa gashi karfi yadda bazai rika karyewa ba. Kudanna kan link din nan Dan samun daman ganin vidiyon yadda ake hada wannan maganin. https://youtu.be/2P-YgHJrX2Q
Friday, 15 May 2020
Monday, 11 May 2020
Friday, 8 May 2020
Sunday, 3 May 2020
Monday, 27 April 2020
Sunday, 19 April 2020
YADDA AKE TURO FILO / DIY FLOWER PILLOW / rahhajs diy
A yau zan koyar da yadda ake dinka filo mai adon fulawa, Ana ado da throw pillow ko turo filo a kan kujeru ko kan gado. Ado da turo filo a yanxu ya zama abin yayi musammam a gidajen amare.
A wannan bidiyon zan koya maku yadda zaku yi throw pillow mai adon fulawa cikin sauki. Domin wannan filon ko bakuda keken dinki kuna iya dinkawa.
Ku danna wannan link din Dan ganin bidiyon yadda ake yi, https://youtu.be/ViyoSQwKq6s
Domin ganin wasu kayatattun bidiyoyinmu dama wasu bidiyon da zaku koyi yadda ake yin sana oin hannu dama gyaran jiki sai Ku bibiyemu ta tasharmu dake YouTube wato rahhaj DIY.
Tuesday, 14 April 2020
GYARAN JIKI / YADDA AKE MAN LEMON TSAMI
Man lemon tsami sinadarine mai matukar mahimmanci waken gyaran jiki musanmam ga masu son su kara was fatarsu haske batare da sunyi anfani da sinadaren kemikal ba Wanda zai iya bata masu fata.
A Wannan karan zan nuns maku yadda zakiyi anfani da lemon tsami wajen gyaran jiki, da hafa mayuka da sabulai, ta hanyar hada naku man lemon tsamin a gida.
ABUBUWAN DA ZAKU NIMA
lemon tsami
Man zaitun
Kwalba
Da farko zaku wanke lemon tsamin sai Ku fere bawon, iya ka Korean, ba a so hada da farin, kamar yadda na nuna a wannan videon https://youtu.be/UK7oEcDHNWg. In kika Tara Wanda zai isheki sai ki juye a kwalba mai Dan fadi irin wannan danai dashi. Sannan sai ki zuba manki akai ki rufe. Ki dakko Leda kisa a ciki ki daure sannan ki binne. Ki barshi tsawon sati 1 ko 2. Da kin dakko zakiga ya juye haka https://youtu.be/UK7oEcDHNWg.
Thursday, 9 April 2020
Sunday, 9 February 2020
HOW TO MAKE CARROT OIL / YADDA AKE MAN KARAS / yadda ake gyaran jiki da ...
yadda ake yin man karas a gida cikin sauki. wannan videon yana kunshe da hanya mafi sauki dan bi a hada man karas. shi dai man karas yanada muhimmanci kwarai wajen gyarn jiki domin ana hadawa dashi a lokacin da ake yin man kitso ko man shafawa da kuma sabulu. domin ganin cikakken videon nan ku danna kan videon ko ku garzaya shafin youtube dina mai suna rahhajs diy.
Friday, 17 January 2020
DIY BAG PACK / YADDA AKE DINKA JAKA / rahhajs diy
YADDA AKE DINKIN JAKAR YAN MAKARANTA
YADDA AKE DINKIN JAKAR YAN MAKARAsai
kuna iya ziyartar shafina dake youtube dan koyan wasu abubuwan da dama da suke can.
Domon ganin yadda zaku dinka jakar makaranta cikin sauki ku danna kan hiton nan.
kuna iya ziyartar shafina dake youtube dan koyan wasu abubuwan da dama da suke can.
Thursday, 2 January 2020
YADDA AKE FILO MAI FULAWA/ HOW TO MAKE FLOWER PILLOW / rahhajs DIY
A wannan video zan nuna muku yadda nai filo mai adon filawa cikin sauki. idan zakui wannan filo din yanada kyau ku samu yadi mai taushi mai kamar yanayin wannn koda baku samu irin sa ba sak. sannan ya kasance mai dan kauri kadan, shine zai bada damar samar da abunda akeso.
wannan filo za a iya dinkawa da zare da allura koda babu keke. domin samun damar koyan yadda zaku hada wannan filo kuma sai ku dannan kan hoton filon ko ku ziyarci shafina da yake youtube dan ganin cikakken videon.
YADDA AKE HADA MAN KITSO
https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs
-
Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa daban daban cikin sauki kuma a cikin gidajenmu...
-
Assalamualaikum yan uwa, a yau Zamu koya maku yadda ake hada man Gyaran jiki da kuma Gyaran Gashi musammam a Wannan yanayin da muke ciki na ...
-
YADDA ZAKU GYARA GASHINKU DA ALBASA Albasa yana da anfani daban daban ciki harda gyaran gashi, kasancewar sa yana dauke da sinadarin su...