Monday, 15 January 2018

YADDA ZAKU HADA MAN GYARAN JIKI DA GASHI LOKACIN HUNTURU

Assalamualaikum yan uwa, a yau Zamu koya maku yadda ake hada man Gyaran jiki da kuma Gyaran Gashi musammam a Wannan yanayin da muke ciki na hunturu.
Wannan mai da Zamuyi bayaninshi a yau yanada saukin hadawa kuma yana gyara fata tai laushi da tsantsi sannan ya Hana fata bushewa da tsatstsagewa a yayin SANYI.

Abubuwan da za'a tanada
Man kwakwa
Man kade
Man habba
Zaitun lauz
Hand mixer
Mazubi.

Yadda ake hadawa
Da farko za asamu wani kwanu sai a zuba man Habba, zaitun lauz, man kwakwa da kuma man kade (Idan an tashi za asa man kade kopi daya, to man kwakwa Rabi za'asa, sauran man kuma sai asa rabi rabin kofi) bayan an hadesu a waje daya sai a samu tukunya a zuba ruwa a ciki kar yakai Rabin tukunyar, sai a Dora akan wuta sannan sai a dakko Wannan kwanun da mukasa sauran mayukanmu a ciki asa cikin Wannan tukunyar. Sannan sai a sa cokali a rika juyawa a hankali a hankali har sai man ya narke. Akula, in za a narka wannan man ba a dorawa akan wuta Kai tsaye inba hakaba za a kashe sinadaren da suke cikin man. Shi yasa ake bin wannan hanyar wajen narkawa.
  Bayan ya narke gaba daya sun hade sai asamu leda a rufe saman kwanun sannan asa a firinji a barshi sai ya Fara daskarewa (zai yi Kamar Kakide) sannan sai a dakko shi a sa mixer a rika gaurayawa Dashi harsai yayi laushi, za aga yayi Kamar kumfa kumfa, Idan mutum baida hand mixer to zai iya sa abin kada kwai irin mai karfinnan yayi ta kadawa Dashi har sai ya hade jikinsa.
Bayan ya hade Sosai sai a juye a wani mazubi mai kyau a rufe. Wannan man kowa zai iya anfani da shi babba da Yaro.

Wannan man yanada matukar anfani wajen Gyaran fata, domin yanasa fata tai laushi, yana cire narkanwa, yana maganin waskanai, yana Hana bushewar fata, yana maganin fashewar lebe, yasa fata sheki da kyau matuka. Sannan yana gyara Gashi yasa tsayi, Baki, laushi da cikowar suma.

Gamai shaawar taga yadda nayi na hada wannan mai tare da adadin danai anfani da sai Ki danna Wannan link din.....  https://youtu.be/3mBJW4V4zkI

Nagode, sai mun hadu a wani darasin.

2 comments:

YADDA AKE HADA MAN KITSO

https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs