Assalamualaikum, yan uwa barkanmu da warhaka, barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku hanyoyi da dabaru na hada abubuwa daban daban cikin sauki acikin gidajenmu.
A yau zan nuna maku yadda zaku sarrafa tsofaffin takardu da jaridu wajen hada tukunyar fulawa a maimakon zubarwa da mukeyi abaya.
Abubuwan da zaku tanada
Takardu /jaridu
Farin gam (top bond)
Tishu (tissue p)
Balo (ballon)
Almakashi
Brushi
Fenti
Kofi
Yadda ake hadawa
Afarko za asamu jaridunne a sa almakashi a yanyanka kanana sai a ajiye a gefe.
Sai kuma a dakko balo din a hura da an girma sai a daure bakin a dorashi akan kicin (wajen kullin a kasa) ku zuba link din DAN ganin abinda nake nufi anan. https://youtu.be/4BXbvsrhP0o
Sai ku dakko wannan gam din kurika shafawa da burushin ajikin balo din, bayan kun shashshafa saiku dauki Takardun nan kubi duk jikin balo din ku Manna, saiku kara shafa gam din akan takardan ku kara bi da takardun ku manne (ku danna link din videon dan ganin abinda nake nufi anan https://youtu.be/4BXbvsrhP0o)
Bayan anyi wannan akalla hawa 5 saikuma a dakko tissue din shima ayi masa kamar yadda akaiwa takardannan. Saina ajiye a gefe abarshi ya kwana saboda ya bushe baki daya.
Bayan ya bushe sai a dakko almakashi a yanke bakin balo din sai kuma akuma sa almakashi a gyara saman wannan tukunya da aka hada. Sannan a shafe/fesheshi shi da fenti, in ya bushe sai a dakko fulawar asa aciki.
Wannan shine yadda zaku Hada tukunyar fulawarku da takardu cikin sauki, duk inda ba a fahimci bayanin da naiba to ayi kokari a kalli videon yadda na hada saboda asamu saukin fahimta, a danna wannan link https://youtu.be/4BXbvsrhP0odin dan ganin videon.
koyi yadda zaka/ki harhada kayan anfanin gida da dabarun kirkirar kayan adon daki harma da sanaoin hannu tare da rahhaj cikin sauki. domin kasancewa damu ku duba youtube channel dinmu dan ganin videos dinmu.
Wednesday, 31 January 2018
YADDA ZAKU HADA TUKUNYAR FULAWA
Tuesday, 30 January 2018
YADDA ZAKU HADA ABUN KWALLIYAR BANGO
Assalamualaikum yan uwa. Ayau ma zamuyi bayani akan yadda zamu hada kayan adon bango wato kayan decoration Na gidajenmu cikin sauki.
Sana'ar decoration sana'ace mai matukar farin jini acikin al'unmam mu a wannan lokaci, sabanin abaya, dayawan mata sun gane sirrin dake cikin gyara tare da kawata gidajensu ta hanyar decoration, wannan yasa a wannan satin bayananmu zasu raba'a akan yadda zamubi mu gyara gidajenmu sannan alokaci guda ku rike wannan harka a matsayin sana'a dan cigabanmu.
Abubuwan da za a tanada
Straw (tsinken lemo)
Spray paint (penti)
Hot glue (gam)
Kwali
Flower
Ribbon/bayis
Yadda zaku hada
Dafarko za a dauki kwalin sai ayankashi yadda zai bada sufar rawun (round) idan an yankashi sai a samu biro a zana wani rawun/circle a tsakiyar wannan kwalin.
Bayan anyi wannan sai a dakko straw din a rika shafa gam din ajiki daga baki bakin sa ana likawa jikin kwalin ta dai dai kan wannan biro da muka zana a tsakiyan kwalin, haka zakuyi ta manna straw din har sai kun zagaye gaba daya jikin wannan kwalin.
To bayan kun jejjera sai kuma ku dakko flowers dinku saiku rika sa gam kuna jejjerawa a saman kwalin DAN ganin yadda zaku hada flowers (FULAWA)din ku danna link dinnan https://youtu.be/Hfq3cI9Ju3w
Bayan kun gama jerawa sai kuma ku dakko pentinku ku feshe gaba daya wannan abun decoration da kukayi. Bayan wannan saiku dauki bayis ko Ribbon ku manna bayan kwalin yadda zaku rika ratayewa jikin bango.
Wannan shine yadda zaku hada wannan abun decoration cikin sauki, dan ganin yadda na hada da kuma kayan aikin danai anfani da saiku duba wannan videon https://youtu.be/XNVLzjOEQdc
Monday, 29 January 2018
YADDA ZAKU HADA ABUN ADON BANGO
Assalamualaikum yan uwa barkanmu da war haka, sannunmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa da Sana'oin hannu a gidajenku kuma cikin sauki.
Ayau zan koya maku yadda zaku hada abin adon bango wato wall hangings/ decor. wannan abun kwalliyar daki yanada matukar kawatawa kuma ana hada shi cikin sauki ba tareda an kashe kudi dayawa ba. Batare da bata lokaciba zaku bukaci abubuwan aiki kamar su.....
Abubuwan da zaku tanada
Cokula Na roba
Madubi (round)
Kwali
Penti (spray paint)
Faranti (circle)
Kyalli (glitters)
Almakashi
Gam (glue gun /stick)
Ribbon (ko bayis)
Yadda zaku hada
Dafarko idan zakuyi wannan abun adon bango zaku nimi cokula na roba sai kusa almakashi ku ciccire kan cokalin https://youtu.be/M1SAEbhAEec. Shi kuma ainihin marikin cokalin sai ku adana (badashi zamuyi anfaniba yau)
Sai Ku dakko kwalinku saiku ajiye akasa sannan saiku dakko faranti ku daura akai kubi jikin farantin da biru (tracing) in kin zana kusa almakashi ku yanka.
Sai Ku dauki wannan kwali da kuka yanka mai zagaye ku ajiye akasa sannan ku dakko madubinku ku daura akai, a daidai tsakiyar (ku tabbata mudubin baikai girman kwalinba) kina iya danna link dinnan dan ganin abinda nake nufi https://youtu.be/M1SAEbhAEec.
Bayan kun sa mudubin kun zana (tracing) a wannan karan bazaku sa almakashi ku yanka ba, sai Ku rika dakko wannan kan cokula da kuka yanyanke ku rika sa gam ta bayan cokalin sannan sai ku rika mannawa ajikin wannan kwalin(zaku fara daga daidai kan layin da kukaja na tsakiyar kwalin) wato dai dai inda zakusa madubin.
Haka zakuyi ta sa gam ajikin cokalin kuna mannawa har sai kun cike duka jikin kwalin sannan sai ku dakko penti ku shafe jikin wannan cokula dashi(har bayan kwalin)
Kafin ku fara fesa pentin yanada kyau ku shin fida kwali akasa saboda karya bata maku waje) bayan kun fesa pentin saikuma ku dakko kyalli ku yaryada akan wannan fenti da sauri kafin ya fara bushewa. Kuna sawa saiku sa gam a daidai tsakiyar kwalin sannan saiku daura mudubin, ku sa hannu kudan danna yadda zai kame.
Bayan kunyi wannan saiku juyo bayan kwalin ku dakko wannan ribbon ko bayis din ku sa gam ku manna da jikin kwalin yadda zai kame ajikin kwalin, to wannan dashi zaku manna abun adon bangon ajikin bango.
Wannan shine yadda zaku hada naku decoration din cikin sauki. Domin karin bayani kuna iya danna wannan link din https://youtu.be/M1SAEbhAEec dan ganin yadda na fara hada wannan abun decoration tundaga farko har karshe. Hakan zai kara baku daman fahimtar komai cikin sauki in sha ALLAH, shi yasa na dauki hoton komai cikin video yadda Za'aga komai. To sai mun hadu a wani darasin.
Wednesday, 24 January 2018
YADDA ZAKU HADA MAN LEBE (LIP BALM)
Assalamualaikum yan uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku darussa akan yadda zaku rika hada abubuwa daban daban da kanku cikin sauki, ayau zan nuna maku yadda zaku hada man lebe da kuma man da zai sanya labbanku taushi da tsantsi in sha ALLAH.
1) lip moisturiser
Abubuwan da zaku tanada
Vaseline ½ cokali
Man kade ½ cokali
Zuma ¼ cokali
Hand dryer
Kwanu
Mazubi
Yadda zaku hada
Dafarko zaku dauki kwanu (bowl)sai ku ibi wannan Vaseline din da man kade ku sanya cikin kwanun saiku dauko hand dryer wato abun busar da gashi, saiku kunna wajen dumin saikuyi anfani dashi wajen narka wannan mai.
Bayan ya narke saiku dakko zuma saiku sa a ciki sannan saiku jujjuya, saiku samu mazubi mai kyau saiku juye aciki. Saiku ajiye kubarshi da ya huce zai kame jikansa.
Wannan mai in kuna shafawa lebenku zai kasance da laushi kuma ya hana bushewa da tsagewa. Dan ganin yadda nai nawa man ku danna link dinnan https://youtu.be/CjfXtbyS4XU . bayan wannan kuma sai dayan man da zan nuna maku kamar haka
2) lip balm
Abubuwan da zaku tanada
Vaseline ½
Man kade ½
Jan baki (kowane kala)
Mazubi
Sai kwanun da za a hada aciki
Yadda zaku hada
Shima wannan kamar wancen wanda mukai ne na farko, zaku dauki Vaseline da man kade ku juye a kwanu saiku sa abin busar da gashi ku narka, idan mutum baida abun busar da gashi zai iya sawa ciki microwave ko ayi anfani da double boiler kamar yadda mukai lokacin da mukayi man gyaran jiki da gashi.
To bayan an narka saikuma a dakko jambaki a gutsiri kadan asa acikin man sai ajuya harsai shima ya narke gaba daya. In anada ragowar jambaki irin wanda ya riga ya kare sai kawai asa abu a dan kwakulo cikin jambakin ayi anfani dashi.
Inya narke sai a juye a robar mai mai kyau abarshi ya daskare a hankali. DAN ganin yadda Nai nawa man saiku Danna link dinnan dan ganin videon https://youtu.be/CjfXtbyS4XU
Wannan shine yadda zaku hada man lebe cikin sauki kuma ya sanya maku taushi da tsantsi a koda yaushe.
YADDA ZAKU HADA MAGANIN GYARAN NONO
Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa daban daban cikin sauki kuma a cikin gidajenmu. Ayau zamuyi magana ne akan gyaran jiki musanmam gyaran nono, ga mai sha'wa ta gyara jikinta ko ta fara hada na sayarwa zata bi wannan hanyar wajen cimma nasarar gyara cikin sauki.
Abubuwan daza a tanada
Garin hulba gwangwani 1
Garin si'itir gwangwani 1
Alkama gwangwani 2
Gyada gwangwani 2
Yadda zaku hada
Dafarko za a fara gyara alkama da gyada a wanke a shanya su bushe sosai sannan sai akai nika a niko su, bayan an niko sai a samu leda mai kyau mai fadi ko faranti babba a bajesu ashanya su sake bushewa sosai.
Sannan sai a samu rariya a tankade a fidda dusan. Shi kuma garin mai laushi sai a samu roba mai kyau sai ajuye aciki.
Saikuma adakko garin hulba da si'itir din shima a hadesu cikin wani roba mai kyau a jiye.
Yadda ake anfani dashi.
Hadin alkama da gyada cokali 2
Hadin hulba da si'itir ½ cokali
Ruwa misalin kopi 1½
Idan aka tashi za ai anfani dashi za a samu ruwa da dan yawa (misali in anaso ayi anfani da ruwa kopi 1ne to sai asa kopi 1½) akan wuta, a dauki cokali a ibi garin hulban da si'itir din nan misalin ½ cokali (ba a'sawa dayawa) sai azuba cikin ruwannan abari ya tafaso.
Agefe guda kuma sai a ibi garin alkamar nan da gyada misalin cokali 2 a danyi kamar za ai talge in ruwan da muka daura a wuta ya tafaso sai a juye wannan kullin da muka dama ai talge dashi (ba'aso yayi kauri) saboda xamu barshi akan wuta saiya dahu, anma fa arikayi ana juyawa saboda karya kama.
In an tabbatar ya dahu sai a juye asamu madara da dan suga asa, sai asha Da dumi. Za a iyayin wannan kullum sau daya, in sha Allah bayan sati 2 ajere za a fara jin/ganin canji.
Monday, 22 January 2018
YADDA ZAKU HADA SHAMPOO A GIDA
Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa da Sana'oin hannu cikin sauki. Ayau munxo maku da yadda zaku hada shampoo da kanku cikin sauki, dan sannin yadda zaku hada shampoo to ku kasance tare da damu.
Abubuwan bukata
Ruwa liter 1
Antisol cokali 3
Sls cokali 1
Caustic soda cokali 1
Soda ash cokali 1
Sulphuric acid cokali 1½
Texapone cokali 3
Methanol ½ cokali
Kala (daidai misali)
Turare
Glycerine cokali 1
Vitamin E cokali 1
Yadda zaku hada
Dafarko zaku samu antisole sai ku samu robar da zaku hada shampoo din aciki ku zuba sanna ku zuba ruwa ku barshi yayi misalin awa 24, in kunaso ma zaku iya barinshi ya kwana 2.
Bayan ya jiku saiku dakko sls din ku juye akai, sannan sai kusa abu ku jujjuya har sai kunga ya hade.
Daga nan saikuma ku dakko Caustic soda sai ku zuba akai, ku cigaba da juyawa harsai kunga ya hade sosai. In kinaso zaku iya jkawa da ruwa kadan kafin ku hadesu.
Saikuma ku dakko soda ash shima ku juye aciki. Shima aita juyawa harya narke.
Saikuma adakko Sulphuric acid shima azuba. Aita juyawa Sosai. Bayan ansa wannan sai a dakko texapone shima ajuye ayi ta juyawa harsai ya hade jikinsa sosai.
To sai kuma ku dakko methanol shima kusa, kucigaba da juyawa inya hade saiku dakko kala (duk wacce kukeso kusa) to saiku jujjuya har sai ya hade gaba daya.
To sai kuma ku dakko turare kusa, ku dako glycerine da vitamin E kusa ku jujjuya shike nan.
Wannan shine yadda ake hada shampoo a gida, DAN ganin yadda na hada nawa saiku danna wannan link din
https://youtu.be/2Qq5Krslk60 dan ganin videon yadda na hada shampoo na daga farko har karshe. To sai mun hadu a wani darasin.
Wednesday, 17 January 2018
YADDA ZAKU HADA AIRFREASHNER A GIDA
Assalamualaikum yan'uwa, barkanmu da sake saduwa a cigaba da kawo maku darussa akan yadda zaku rika hada abubuwa daban daban da kanku a cikin gidajenku, a yau Zan nuna maku yadda zaku hada airfreashner ne Wato turaren daki cikin sauki.
Abubuwan da za'a tanada
Ruwa liter 1
Texapon cokali 3
Methanol Rabin Rabin liter
Turare (lavender)
Kala
Mazubi
Yadda zaku hada
Datar zaku samu roba mai fadi, Wanda za mu hada komai aciki, sai a dakko texapone a sa aciki sannan a dakko Wannan methanol din a juye akai, sai asa abu a jujjuya har sai ya hade gaba daya.
Sai kuma a dakko ruwan sai a juye akai, shima a jujjuya, bayan an juya ya hadu sai a dakko kalar da akeso ayi anfani da, ni nayi anfani da ruwan hodane, sai a sa a wani robar a sa ruwa kadan yadda zai narke kafi a juye a Cikin wanan hadin turare da mukeyi.
Bayan an juye sai kuma a dakko turaren (zaku iya sa Wanda kuke so shima) bayan kunsa sai Ki jujjuya Sosai sannan sai ku samu mazubi irin na turare Ku juye aciki, Shike nan.
Ga Wayanda suke da sha'awar suga yadda na hada nawa turaren Ku danna wannan link din Dan ganin videon https://youtu.be/LOSMy8fy2cs
Nagode.
Tuesday, 16 January 2018
YADDA ZAKU HADA SABULUN WANKE WANKE (LIQUID SOAP)
Assalamualaikum yan uwa matasa, a yau zamu koya maku yadda ake hada sabulun wanke wanke Wanda aka fi Kira da liquid soap.
Abubuwan da za'a tanada
Nitrosol
Caustic soda
Soda ash
Sulphuric acid
Texapon
Kala
Turare
Ruwa lita daya
Mazubi
Yadda ake hadawa
Dafarko Idan za ai Wannan sabulun, za asamu roba mai fadi, sai a dauki cokali a auna nitrosol cokali 2 a zuba acikin wannan robar mai fadin, sai a dauki wannan ruwan a rabashi gida 2,azuba Rabin acikin nitrosol din Rabin kuma sai a ajiye a Gefe. Sai a samu wani abu a rika jujjuya wannan nitrosol da muka zuba ruwa a ciki har sai ya narke.
Sai kuma a samu wata robar karama a ibi ruwa daga cikin Wannan ragowar da muka ajiye, sai a zuba acikin wannan karamar roba sannan a ibi caustic soda Rabin chokali azuba aciki, sai aita juyawa har sai ya narke. Sannan sai a juye a cikin Wannan roba mai fadi Wanda muka sa nitrosol a ciki, sai kuma Acigaba da juyawa.
Bayan sun hade sai kuma a ibi soda ash cokali 2 a zuba a Wannan karamar roba, a ibi ruwa kadan daga cikin Wannan Wanda muka rage a zuba akan soda ash din asa abu ajuya. In ya narke sai shima a juye akan nitrosol din nan na cikin robar nan mai fadi. Sai Acigaba da juyawa.
To sai a dakko sulphuric acid a ibi cokali 2, a zuba acikin wannan robar mai fadi na nitrosol Acigaba da juyawa.
Sai kuma a dakko texapone a ibi cokali 2 a asa a Wannan karamar roba sannan sai azuba wannan hadin nitrosol din akai, ana juyawa (za aga yana kauri) to sai arika karawa kadan kadan ana juyawa, in Kaurin ya daidaita sai a juyeshi acikin robar nitrosol din Acigaba da juyawa. Har sai anga gaba daya ya Hade waje guda.
To sai kuma a dakko kala, asa iya adadin da akeso acikin wannan karamar robar sai kuma ajuye ragowar ruwan munnan akai, ajuya Sosai sannan sai ajuye akan Wannan hadin nitrosol din, ajujjuya sannan daga karshe sai asa turare, shima za'asa dai dai yadda ake so, sai ayita juyawa har ya hade gaba daya.
To in ya hadu Sosai Sai a samu mazubi mai kyau sai ajuye. Wannan shine yadda zaku hada sabulun wanke wanke (liquid soap) agida, ga masu sha'awan suga yadda na hada nawa sabulun sai su danna wannan link din Dan ganin cikakken videon https://youtu.be/g-aNZRkiDxg
Monday, 15 January 2018
YADDA ZAKU HADA MAN GYARAN JIKI DA GASHI LOKACIN HUNTURU
Assalamualaikum yan uwa, a yau Zamu koya maku yadda ake hada man Gyaran jiki da kuma Gyaran Gashi musammam a Wannan yanayin da muke ciki na hunturu.
Wannan mai da Zamuyi bayaninshi a yau yanada saukin hadawa kuma yana gyara fata tai laushi da tsantsi sannan ya Hana fata bushewa da tsatstsagewa a yayin SANYI.
Abubuwan da za'a tanada
Man kwakwa
Man kade
Man habba
Zaitun lauz
Hand mixer
Mazubi.
Yadda ake hadawa
Da farko za asamu wani kwanu sai a zuba man Habba, zaitun lauz, man kwakwa da kuma man kade (Idan an tashi za asa man kade kopi daya, to man kwakwa Rabi za'asa, sauran man kuma sai asa rabi rabin kofi) bayan an hadesu a waje daya sai a samu tukunya a zuba ruwa a ciki kar yakai Rabin tukunyar, sai a Dora akan wuta sannan sai a dakko Wannan kwanun da mukasa sauran mayukanmu a ciki asa cikin Wannan tukunyar. Sannan sai a sa cokali a rika juyawa a hankali a hankali har sai man ya narke. Akula, in za a narka wannan man ba a dorawa akan wuta Kai tsaye inba hakaba za a kashe sinadaren da suke cikin man. Shi yasa ake bin wannan hanyar wajen narkawa.
Bayan ya narke gaba daya sun hade sai asamu leda a rufe saman kwanun sannan asa a firinji a barshi sai ya Fara daskarewa (zai yi Kamar Kakide) sannan sai a dakko shi a sa mixer a rika gaurayawa Dashi harsai yayi laushi, za aga yayi Kamar kumfa kumfa, Idan mutum baida hand mixer to zai iya sa abin kada kwai irin mai karfinnan yayi ta kadawa Dashi har sai ya hade jikinsa.
Bayan ya hade Sosai sai a juye a wani mazubi mai kyau a rufe. Wannan man kowa zai iya anfani da shi babba da Yaro.
Wannan man yanada matukar anfani wajen Gyaran fata, domin yanasa fata tai laushi, yana cire narkanwa, yana maganin waskanai, yana Hana bushewar fata, yana maganin fashewar lebe, yasa fata sheki da kyau matuka. Sannan yana gyara Gashi yasa tsayi, Baki, laushi da cikowar suma.
Gamai shaawar taga yadda nayi na hada wannan mai tare da adadin danai anfani da sai Ki danna Wannan link din..... https://youtu.be/3mBJW4V4zkI
Nagode, sai mun hadu a wani darasin.
Wednesday, 10 January 2018
YADDA AKEYIN MAN KWAKWA (2)
Abaya munyi bayanin akwai hanyoyin yin man kwakwa daban daban har mun koyar da yadda ake bin hanya ta farko wajen yin man kwakwa a gida, ayau kuma zamu koya maku daya hanyar in sha Allah.
ABUBUWAN bukata:
Kwakwa
Ruwa
Wuka
Abin kankara
Abin markade
Tukunya
Yadi ko rariya
Mazubi.
Yadda akeyi:
Dafarko in za Ai man kwakwa za a Fara bare bawon kwakwarne, sannan sai a wanke kuma kankare wannan DAN jajajan jikin kwakwar, bayan an kankare sai adau wuka a yanyanka ta kanana.
Bayan an yanmata sai a zuba a abin markade a zuba ruwa wadatacce sannan sai a markada har sai ya yi laushi. Sannan sai a dakko yadin Tatar koko ko rariya mai laushi a tace wannan markade, sannan sai a juye ruwan kwakwar a wani mazubi mai fadi a saka cikin gidan firinji.
Idan za asa ba a sawa a gidan kankara, saboda banason ya kankare, za a barshi ciki harsai anga ruwan ya rabe 2, Wato ruwan kwakwar yai kasa man kwakwar tai sama.
Sai a dakko a yade wannan man kwakwar data kwanta a sama sannan sai a sa cikin tukunya a Dora akan wuta. Sai a rika juyawa LOKACI LOKACI har sai anga ya Fara curewa, kula za aga mai ta Fara tsatstsafowa, sai a rage wuta acikagaba da juyawa harsai wannan tika tika ta cure duka, sai a sauke abarshi yasha iska, sannan sai a tace a juye a mazubi Shike nan.
Dan ganin yadda na yi nawa man kwakwar daga farko har karshe ku danna wannan link din https://youtu.be/hFyKsPh5Qrg ko Ki danna hoton man kwakwar.
YADDA AKE YIN MANKWAKWA
Assalamualaikum yan'uwa, ayau zamu koya maku yadda ake yin MANKWAKWA a gida.
Idan za Ai man kwakwa ana iya bin hanyoyin da dama wajen fidda man daga jikin kwakwa, anma ayau Zamuyi muku bayani akan yadda ake yinsa ta hanyoyin biyu in sha Allah.
hanaya ta farko (1)
Abun da zaku tanada:
Farin kwakwa
Wuka
Ruwa
Abin markade (blender)
Yadi ko rariya
Tukunya
Mazubi
Yadda ake yi:
Da farko zaku sami farin kwakwa, saina bare bawon sannan sai a yanyanka kanana yadda zai mana dadin markadawa.
Bayan mun yanka sai mu wanke sannan sai asa a abin markade a zuba ruwa wadatacce a markada sai yayi laushi.
Bayan an markada sai adau rariya mai laushi ko yadi irin na Tatar koko sai a tace wannan ruwan kwakwa da muka markada.dusar kuma in Anaso za a iyayin kwakumeti ko biskit Dashi.
Shi kuma wannan ruwan kwakwa sai a juye a tukunya a Dora akan wuta a barshi yayita tafasa (Anma kar a rufe tukunyar). Haka za a barshi harsai ruwan ya Kare gaba daya za a GA mai ya Fara fita, Sai a rage wutar a hankali za aga gaba daya ruwan ya kone.
Sai a kashe wutar abari ya huce sannan sai a dau rariya ko wani yadi mai kyau sai a tace. Sai a dau man da aka tace asa ajuye a mazubi, dattin da aka tace kuma sai a zubar.
Tuesday, 9 January 2018
RAHHAJ'S HOME MADE INSPIRATIONS
Assalamualaikum yan uwa mata da maza, Rahhaj's na farincikin Sanar maku da cewar sun bude sabon channel dinsu a YouTube inda suke koyarda sana'oin hannu iri daban daban, Kama daga Dinkin kayan sawa, zannuwan gado, labulaye, takalma, jakunkuna, yari da sarka, dinkunan yar kanti ta yara, hada kayan kwalliyar gida Kamar kayan adon bango, kayan ado na daki, bandaki da kayan afani na jarirai.
Bayan wayannan zamu rika koyarda kayan Gyaran jiki Kamarsu man shafawa, sabulai, turaruka, da wasu abubuwan da dama, kudai Ku kasance damu Dan cin moriyar Wannan Garabasar.
Domin kasancewa damu a channel dinmu na YouTube (rahhaj's home made inspirations) ku biyo Wannan link din
>>> https://www.youtube.com/channel/UCrl5ZMZofMdca6cHvwmT2_A
YADDA AKE HADA MAN KITSO
https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs
-
Assalamualaikum yan'uwa barkanmu da sake saduwa Acigaba da kawo maku dabarun hada abubuwa daban daban cikin sauki kuma a cikin gidajenmu...
-
Assalamualaikum yan uwa, a yau Zamu koya maku yadda ake hada man Gyaran jiki da kuma Gyaran Gashi musammam a Wannan yanayin da muke ciki na ...
-
YADDA ZAKU GYARA GASHINKU DA ALBASA Albasa yana da anfani daban daban ciki harda gyaran gashi, kasancewar sa yana dauke da sinadarin su...