Sunday, 2 January 2022

YADDA AKEYIN SABULUN WANKI

YADDA AKE SABULUN WANKI (LAUNDRY BAR SOAP)

Ayau zan koya maku yadda zakuyi sabulun wanki da kanku cikin gidajenku ba tare da kun kashe kudi dayawa ba, ko kuma kun nimi Mayan aiki masu tsada. Abinda zaku Nina kawai anan shine yakan da zakuyi amfani da, robobin aikinku sai kuma safar hannu sabida kariya.

ABUN BUKATA
Soda ash
Caustic soda
Silicates starch
Man P.K.O
Turare

YADDA AKE HADAWA

A samu bokitin roba na fenti ko baho karami sai a iba garin caustic soda da soda ash a jikasu, anma kowannensu daban za'a iba. sannan sai a zuba ruwa a jikasu, abarsu su kwana a ruwan.

Idan za'a hada sai a fara samun wata robar mai Dan fadi a juye man pko din, sannan sai a dakko sannan caustic soda din da aka jika a juya da cokalin roba ko na katako sannan sai a juye akan wannan man.

Ana juyawa sai a dakko shima soda ash din a juya sosai sannan a juye shi ana juyawa, sai kuma asa silicate starch da turare. In ya hade sai ki dauko robar da zaki zuba, in kuma kinada molin yin sabulu sai ki juye a ciki.

In aka juye za'abarshi sai ya hade kafin a cireshi, sannan yanada kyau asa safar hannu kafin a fara, idan kuma anaso asa kala ana iya sawa.
Sannan adadin kayan hadin zai zama iya adadin yawan da ake bukata. Ashawarce in akaje sayen kayan hadin sai afadi masu adadin da za a hada Dan su auna daidai bukata.

Karku manta kuna iya bibiyar shafinmu na YouTube Wanda acanne Mike nuna komai cikin video, da kuma Facebook group dinmu Wanda acanma muna koyar da wash abubuwan. Dukkansu sunansu (Rahhaj's DIY)

Allah yakawo kasuwa mai albarka.

No comments:

Post a Comment

YADDA AKE HADA MAN KITSO

https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs