Tuesday, 6 March 2018

YADDA ZAKU DINKA TUM-TUM (1)



Assalamualaikum yan uwa, barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa a cigaba da kawo maku dabarun harhada abubuwa da kanmu acikin gidajenmu kuma acikin sauki . Ayau zamuyi bayani ne akan yadda zakuyi tum tum, wato manyan filo wanda ake ajewa a cikin daki akasa. Wannan tumtum kala kala ne amma zamu fara bayani akan wanda yafi ko wanne sauki in yaso daga baya, sai muyi bayani akan sauran in sha Allah.

Abubuwan da za'a tanada
Yadin kujera ko wani yadi mai dan kauri
Fiber ko crumbs (soson katifa)
Tape
almakashi
Zip
Yadda zaku dinka
Dafarko zaku fara auna iya girman da kukeso wannan tumtum ya kasance. Misali ni anawa nasa tsayi inci 22 fadi kuma inchi 20. To kuma kuna iya sa hakan ko ku kara ko ku rage.
Sai ku sa almakashi ku yanka dai dai abinda kuka auna, inkun tashi yankawa zakunyanki guda 2 ne, wato gaban filon da bayan. sannan saiku hadesu biyun. Ku kama saman ku dan dinke, kasanma ku kama ku dinke (misalin inci 2) akwai video da nayi dan karin bayani sai ku danna wannan link din https://youtu.be/J56Dvtm4gdo dan ganin yadda zaku kama ku dinke.
Bayan kun dinke saiku bude wanan yadi yadda zai tashi guda daya. To anan zakuga tsakiyan yadan bude kamar fuskar nikabi. To tanan ne zamu saka zip. Yanzu sai a dakko zip din a sanya ta kasan wannan fuska da mukai a kama gefe gefen a hada da jikin zip din a dinke. (wanan waje yanada wuyar bayani da baki shi yasa na aje link dan kuga abinda nake nufi yayin dinkewa https://youtu.be/J56Dvtm4gdo. Ku danna kuga yadda nasaka zip din)
To bayan ansa zip din saiku juya yadin abaibai ku take ragowar gefen guda uku. Zakuga ya hade ya baku suffar pillo. To saiku bude zip din ku juyo da shi dai dai. To anan zaku iya anfani da fiber ko foam wajen duri, sannan zaku iya sa fiber kai tsaye aciki ko ku fara dinka wani gidan pilon ku dura fiber aciki kafin kusa acikin tumtum din. Sannan in kunaso zaku iya samun foam inci daya ku manne gefen guda hudu da gam ku dura crumbs aciki (ku duba videon na nuna wannan kalan)
  To da kunyi wannan shikenan sai ku zuge xip dinku. Shi 4thum tum anayinsa hawa hawane, kamar hawa 2,3 ko 4. Ya dangsnta da raayin maishi. To in kun tashi zakuy karamin wannan saiku rage inchi 3 zuwa 5 akan wannan awon da na baku, in kuma zakuyi banbansa saiku kara inchi 3 zuwa 5 akan awon.
Wannan shine yadda zakuyi tum tum.mai sauki. Karku manta ku danna wannan link din dan ganin komai acikin video. https://youtu.be/J56Dvtm4gdo

Monday, 5 March 2018

YADDA ZAMU GUJEWA KURAJEN FUSKA (PIMPLES)




Assalamualaikum yan uwa munai maku barka da kara kasancewa damu. In sha Allah yau zamu dora bayaninmu da mukeyi akan kurajen fuska, a baya mun nuna hanyar da muyi mu magance kuraje a fuskarmu, ayau kuma kamar yadda na alkawarta zanyi bayani akan abubuwan da ya kamata mu kiyaye domin ganin mun rabuda kurajen da suke damun mu in sha Allah.
1) YAWAITA WANKE FUSKA
dayawanmu muna da dabi'ar yawaita wanke fuskokinmu akai akai, wasu sukan wanke fuskarsu a rana akalla sau 6 ko fi kuma da sabulu. Wannan dabi'a tana kara janyo mana kuraje a fuskarmu saboda wayannan sinadaren da suke cikin sabulun suna wanke ainihin maikon da Allah ya sanya fata ta kasance ciki sannan su sa fata bushewa da kuma darewa.
  Abinda ya kamata mu yi shine indai zamusa sabulu a fuskarmu to akalla mu wanke sau 2 kawai (safe da yanma/dare).
2) ANFANI DA SABULU MAI KARFI
dayawanmu mukan yi anfani da sabulu wanda yafi karfin fatarmu, misali medicated ko lightening soap. Wayannan suna dauke da sinadaren da suke kara sanya wa fuska ta samu matsalar fata musanmam ga wayanda dama can sunada pimples a fuskarsu, maimakon wayanan sabulai zaifi kyau mu samu sabulu wanda yake baida karfi sosai (beauty soap kamar joy, giv, dov, lux etc) anma matukar zamu cigaba da anfani da sinadarai masu karfi akan fatarmu to ko muna maganin kuraje, zasu rika tafiya suna dawowa.
3) MAN SHAFAWA MAI KARFI
man shafawa kamar sabulu shima, yana dakyau mu nimi wanda yayi daidai da yanayin fatarmu. Misali in fatarmu mai saurin bushewa ce to yana da kyau mu nimi man shafawa mai dan maiko wanda zai rika hana fatarmu saurin bushewa da tsagewa. Haka in fatarmu mai maikoce, to zaifi kyau muyi anfani da mai wanda baya daskarewa jikin fuska saboda fatar ta samu damar shan iska yanda ya kamata.
4) KWARZANE FUSKA /FASA PIMPLES
wannan dabi'a ita tafi saurin janyo mana matsalar kuraje da kuma tabbuna a fuskokinmu, dayawan masu fama da pimples basa rabo da wasa da hannunsu akan fuskokinsu, kodai suna shafa fuskar ko kuma suna fasa pimples din ko suna kwarzane kurajen. Wannan yanasa kwayoyin cututtka saurin shiga fata wanda yana daya daga cikin dalilan da suke kawo pimples, sannan yana sa kurajen suyi baki su bar mana alamar tabo wanda yakan dauki lokaci kafin ya fita.
5) RASHIN WANKE HANNAYE AKAI AKAI
Barin dauda ajikin hannu yana taimakawa matuka wajen kara jawo mana pimples a fuskokinmu, shi yasa yake da kyau mu rika wanke hannayenmu kafin mu shafa mai ko wani maganin kuraje saboda da tafin hannunu muke yin kusan komai kama daga shara, ayyukan gida, taba wayoyinmu da dai sauransu,shiyasa in muna wanke hannu akai akai sai mu guji karawa ciwo ciwo.
6) RASHIN GYARAN FUSKA (DILKA)
Rashin gyaran fuska wanda zai taimaka wajen cire duk wani dauda da take kan fatar mu na taimakawa wajen kara jawo mana kuraje, kamar yadda yawaita yin gyaran fuskarma zaibiya kara mana pimples a fuskokinmu. Dilka ko exfoliating hanyace da akebi wajen cire duk wani datti da mataccen fata wanda baida anfani akan fatarmu, ta yadda fatar tamu zata kasance da kyau, sheki, tsantsi da lafiya a koyaushe. Shi yasa yake da kyau mu rika yawaita yin wannan akalla sau daya a sati domin mu hana sabbin kuraje baiyana a fuskokinmu.
7) YANAYIN ABINCHI
Abincin da muke ci yana daya daga cikin abinda yake kara jawo mana kuraje a fuskokinmu, kamar yadda mukasani yawaitar maiko a karkashin fata na daya daga cikin dalilan da suke kawo mana kuraje, shi yasa yake da kyau mu rika ragewa koda bazamu iya daina cin nauoin abinchin da suke dauke da maiko mai yawa wanda suke jawo mana pimples ba. Misalin abincin su hadar da kayan zaki irinsu cake, doughnuts, da dai sauransu, sai kuma masu maiko kamar gyada, magerine da dai sauransu.
8) SHIGA RANA
Yawaita shiga rana na daya daga cikin dalilan da yake sawa muyita maganin pimples anma yaki tafiya koda kuwa muna bin dokoki muna kiyaye cimarmu. Shiyasa mafi akasarin masu fama da pimples yan matane wayanda suke yawaita fita makaranta, aiki da dai sauransu. Yana da kyau in za a fita cikin rana kar a shafa mai wanda yake da maiko sosai (oil) ko kuma ayi anfani da man kariya (sunscreen)
9) YANAYIN HALITTA
Bayan duk wayannan dalilai dana lissafa a sama akwai kuma wanda dama halittarsu ce kurajen fuska, wannan kuma yana faruwa ne saboda rashin daidaitar sinadaren halitta na jiki (homones) shiyasa wasu za kuga suna iyakar kokarinsu wajen kiyaye duk wayannan sharudodi anma duknda haka pimples baya rabuwa da fuskokinsu. Wayannan abunda ya kamata shine su nimi likita dan ya sanar masu da kwayoyin da ya dace suyi anfani da shi wajen magance matsalar.
10) LOKACHI
Pimples lokacine kamar yadda dayawan mutane suke fada, koda yake wasu harda rashin kiyayewa da bin sharrudan da na lissafa, anma mafi akasarin lokuta pimples yana zuwa ne dai dai lokacin da matasa suke samun yanayin canji na girma a halittarsu :puberty
Sai dai wasu daga nan ne kuma in basa kiyaye sharudan nan na sama sai su wuce dashi har girma.
11) BLEACHING
Bleaching ko shafe shafe na daya daga cikin manya manyan dalilan da suke kawo kuraje jikin fuska, kuma wannan shi yafi ko wanne muni domin shi zai futo manya manya sannan yasa fuskar tai jirwaye ta kuma yi tabbuna ko ina, shi yasa yana da kyau mu guji anfani da duk wani mai ko sabulu da zai sanyamu haske domin suna kona mana fatane kawai su kuma baiwa cututtuka damar shigar mana fata.
Wayannan sune kadan anma kuma manya manyan dalilan da suke jawoana kuraje a fuska ya zamana munata magani anma bama samun canji, da fatan zamu kiyaye. In sha Allah nan gaba zamuyi bayanin kalolin dilka da yadda zamu hadasu da kanmu cikin sauki .

YADDA AKE HADA MAN KITSO

https://youtu.be/YQ3YQAbIIHs